Yadda azabtar da ɗalibai a makarantu ta zamo annoba a Kenya

Ɗalibin da aka azabtar a marakata a Kenya
Bayanan hoto, Ɗalibin da aka azabtar a marakata a Kenya
    • Marubuci, Daga Tom Odula a Nairobi & Tamasin Ford a London
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sashen BBC Africa Eye mai binciken kwakwaf
  • An wallafa

An yi wa Caleb Mwangi dukan kawo wuka a makarantarsu da ke Kenya bayan ya ɗebi abinci fiye da kasonsa a lokacin karin kumallo, har sai da ya yi dogon suma, kuma ya shafe kwana 11 a gadon asibiti.

"Lokacin da na isa wurin, ba zai iya sauka daga gadonsa ba, ba ya iya magana," mahaifinsa Fred Mwangi ya shaida wa BBC.

Hakan ya faru kusan shekaru biyu da suka gabata lokacin da Kaleb yana ɗan shekara 13. Yanzu ya na zaune a tsakanin iyayensa a kan kujera a gidansu da ke birnin Mombasa, wani birni da ke gaɓar tekun Kenya, ya ce yakan suma daga lokaci zuwa lokaci.

Matashin na cike da bacin rai wanda wani lokaci yakan sa shi ya naushi bango. Ya ce ido-biyu da ya yi da mutuwa ya yi tasiri a kan shi sosai.

Mista Mwangi ya sa ɗansa ya tashi ya cire farar rigar da yake sanye da ita don ya bayyana wani tabo mai kauri wanda ya mamaye kusan fadin bayansa.

Ya ce raunukan sun yi zurfi sosai har sai da likitan ya yanko fata daga cinyoyinsa domin yin dashen fata a kan raunukan.

Zalunci a makaranta
Bayanan hoto, Zalunci a makaranta

"Wannan shi ne lokacin da ya ke asibiti," in ji mahaifiyarsa Agnes Mutiri, tana nuna hotunan Kaleb a wayarta, wanda ba za a iya wallafawa ba. Ya na kwance rub-da-ciki a kan gado, raunuka sun rufe ƙafafunsa da baya da hannayensa, har ma da fuskarsa. Akwai kusan guda ɗari gaba ɗaya.

"Jikinsa duka haka yake."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Azabtar da yara a makarantu yana da dogon tarihi a Kenya, tun daga zamanin da turawa da masu mulkin mallaka suka dogara da shi don tabbatar da ikonsu.

A shekara ta 2001, gwamnatin Kenya ta haramta yin hakan a makarantu, amma da wuya a iya sauya tunanin mutane.

Alƙaluma daga sabon rahoton cin zarafin yara, wani bincike a shekarar 2019, ya nuna cewa fiye da rabin matasa masu shekaru 18 zuwa 24 a Kenya sun yarda cewa ya zama dole malamai su yi amfani da irin wannan nau'in horon.

Sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya bankaɗo yadda ake samun ƙaruwar aukuwar ire-iren waɗannan lamuran.

Caleb ya ce Nancy Gachewa, daraktar Cibiyar Ilimi ta Gremon - wata makaranta a garin Bamburi da ke kusa da Mombasa - ce ta fara lakaɗa masa duka sannan ta umarci sauran ɗaliban da su ci gaba da hukunta shi.

Ms Gachewa ta musanta hakan, kuma ta ce ba ta cikin makarantar a lokacin da abin ya faru.

"Ina jin yunwa sosai, sai na ɗauki chapatis guda biyar na cinye su da shayi," in ji Kaleb.

An kama Ms Gachewa da wani babban ɗalibi, Idd Salim, kuma an tuhume su da laifin cin zarafi da kuma cutarwa ta hanyar raunatarwa.

A shekarar da ta gabata ne dai aka yanke wa Salim hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari, kuma a wata yarjejeniya tsakaninsa da hukuma, ya bayar da shaida kan Ms Gachewa a kotu. Ana ci gaba da shari'ar da ake mata.

Duk da yake lamarin Kaleb yana da ban tsoro, ba abin da ba a saba gani ba ne. Wani ma'aikaci a Hukumar Kula da Malamai (TSC), wata ƙungiya mai zaman kanta da ke kula da duk wani nau'i na aikin koyarwa a Kenya, ya yi magana da BBC Africa Eye bisa sharaɗin sakaya sunansa.

Zalunci a makaranta
Bayanan hoto, Hukumar ta TSC ta goyi bayan wani shiri na horar da malamai yadda za su ba da horo ba tare da yin amfani da hukuncin kisa bsun azabtar da yara ba

Sun ce a cikin shekaru uku da suka gabata, rahotannin azabtarwa mafi muni a makarantu sun ruɓanya fiye da sau huɗu, daga bakwai zuwa 29. Yawancin irin wadannan lamuran da ke faruwa ba a kai rahotonsu.

"Ba ƙaramin bala'i ba ne kuma… muna ganin abin na neman wuce gona da iri yanzu. Al'amuran da suka shafi ƙananan yara da aka raunata. Wasu daga cikin waɗannan al'amura sun haifar da munanan sakamako, har ma da mutuwa," in ji su.

Majiyar ta ce, lamarin azabtar da yara a makarantu da aka sanarwa hukumar ta TSC a matakin ƙananan hukumomi ba a ɗaukar wani mataki a kai, inda ta ƙara da cewa akwai batutuwan da ba a bari sun yi tasiri ba”.

"Sau da yawa, a lokacin da shari'ar ta iso gare mu, an gurɓata hujjoji da yawa, wani lokacin ma ba ma iya samun shaidu."

BBC Africa Eye ya tuntuɓi hukumar ta TSC domin amsa waɗannan zarge-zargen, amma ba ta mayar da martani ba.

Tunanin cewa dalibi zai iya mutuwa a hannun ƙwararrun malamai da ya kamata su ba su kariya, abu ne da ba ya iya misaltuwa ga mafi yawan mutane, amma a cikin shekaru biyar da suka gabata kafafen yaɗa labarai sun bayar da rahoton mace-mace sama da 20 da ake dangantawa da duka a makaranta.

Ebbie Noelle Samuels

Ana tunanin cewa Ebbie Noelle Samuels mai shekaru 15 tana cikin su.

Ebbie ɗalibar kwana ce a makarantar sakandare ta Gatanga CCM da ke gundumar Murang'a, mai tazarar kilomita 60, da ke arewa maso gabas da babban birnin ƙasar, Nairobi.

A ranar 9 ga Maris 2019 makarantar ta kira mahaifiyarta, Martha Wanjiro Samuels, aka faɗa mata cewa 'yarta ba ta da lafiya a asibiti.

Lokacin da ta isa wurin, Ebbie ta riga ta mutu.

Makarantar ta ce ɗalibar ta mutu ne a cikin barci, amma shaidu sun ce mataimakiyar shugaban makarantar ce ta lakaɗa mata duka saboda yanayin gyaran gashin da ta yi a kanta.

"Rahotan binciken da aka gudanar kan gawar ya nuna cewa ta samu mummunan rauni a kai. Don haka, wani ne ya buge ta har ya yi mata irin wannan raunin, wanda ya kai ga mutuwarta," in ji Mrs Samuels.

Ta yi fafutuka na tsawon shekaru huɗu don a binciki mutuwar ɗiyarta.

A watan Janairun da ya gabata, an kama Elizabeth Wairimu Gatimu, tsohuwar mataimakiyar shugaban makarantarsu Ebbie da laifin kisan kai. Ta dai musanta zargin da ake mata.

"Zan yi duk abin da ya kamata in yi muddin ina raye don ganin an yi wa 'ya ta adalci," in ji Misis Samuels, wacce har yanzu take jiran jin sakamakon shari'ar.

"Na gaya wa kaina: 'Ba za a rufe min baki ba, ba zan yi shiru ba, ba zan daina faɗa ba." Watakila ranar da na haƙura ita ce ranar da na yi barci irin ta 'ya ta, amma muddin ina numfashi ba zan daina ba."

BBC Africa Eye ta bukaci tattaunawa da ma'aikatar ilimi ta Kenya, amma babu wanda ya yarda ya yi magana.

Wata ƙungiya da ke neman sauyi ita ce Beacon Teachers Africa. Ƙungiyar mai zaman kanta wanda Plan International ta ƙaddamar a ƙasar Kenya shekaru huɗu da suka gabata, tare da TSC, manufarta ita ce baiwa malamai damar kare yara a makarantu da kuma yankunansu.

Yanzu tana da alaƙa da malamai 50,000 da ke ƙasashe 47 na Afirka.

Zalunci a makaranta

Robert Omwa yana ɗaya daga cikin malaman Beacon 3,000 a Kenya. Baya ga ilmantar da yara game da haƙƙoƙinsu, yana kuma gudanar da bita don horar da malamai yadda za su ba da horo ba tare da sun azabtar da yara ba.

"Da farko na yi shakku game da hakan, na ɗauka wannan aƙidar ƙasashen yamma ce, dole ne a yi wa yaro dan Afirka duka. Amma da na gwada hakan, sai na ji sauƙi a matsayina na malami, na ji hankalin yaran na karkata zuwa wuri na ." Ya ce.

Idan muka koma Mombasa, inda Caleb da iyalinsa ke jiran su ji makomar daraktan makarantarsa. Ms Gachewa wanda ta musanta aikata laifin.

Dan shekaru 15 din har yanzu yana fuskantar ƙalubale wurin hakura da abin da ya faru da shi.

"Don a yi mun adalci, ina son a ɗaure wannan matar."