Mece ce illa da kuma alfanun ƙarin albashi ga ma'aikata?

    • Marubuci, Daga Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • An wallafa

'Yan magana kan ce duk abin da ya yi amfani tabbas zai yi rashin amfani.

Sai dai idan aka yi maganar ƙarin albashi, ma'aikata ba su maraba da ɓangaren farko na wannan maganar - toshe kunnensu kawai suke yi har sai sun ji ƙarin sai a yi maganar daga baya.

Ba su da laifi ko kaɗan saboda da ma masana tattalin arziki na cewa amfanin ƙarin albashin ya rinjayi rashin ƙarin a mafi yawan lokuta.

A Najeriya dai tuni gwamnatin tarayya ta ce ta ƙara wa ma'aikatanta albashin da kashi 25 zuwa 35. Amma har yanzu ana ci gaba da jiran abin da gwamnatin za ta yanke game da mafi ƙarancin albashi, wanda da shi ne ƙananan ma'aikata za su san matsayar albashinsu a ƙasa ɗaya.

Hauhawar farashi ta kai kashi 33.20 cikin 100 a watan Maris, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta bayyana, kuma shi ne adadi mafi yawa cikin shekara 28.

Yayin da duk wannan ke faruwa, masana na cewa ba ƙarin albashi kawai ya kamata gwamnati ta saka a gaba ba, hasali ma da an ɗauki wasu matakai ba sai an kai ga ƙarin ba.

Wannan ta sa muka duba irin alfanun da ma'aikatan za su samu ko akasin haka idan suka fara jin ƙarin a aljihunsu.

'Ba ma'aikata ne kawai za su ci amfanin ƙarin ba'

Duk lokacin da aka yi maganar ƙarin albashi waɗanda ba ma'aikata ba sai su ji cewa "mu kuma fa?!".

Masana tattalin arziki na cewa amfanin da ke tattare da ƙarin albashin ba ma'aikata kaɗai zai shafa ba saboda yanayin zamantakewar da ake ciki.

A tsarin tattalin arziki akwai abin da ake kira "factor income" a Turance - wato kusurwa huɗu ta zagayawar arziki a tsakanin al'umma, a cewar Dr Abdussalam Abubakar na Sashen Tattalin Arziki a Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua da ke jihar Katisna.

"Na farko shi ne kuɗin da ma'aikaci yake samu [albashinsa], idan ya biya kuɗin haya to shi ma mai gidan hanyar samunsa kenan," in ji masanin.

"Sannan idan ma'aikacin ya je kasuwa ko kuma ya biya kuɗi aka yi masa wani aiki, ya ƙara samar wa wasu arziki kenan. Haka nan idan samunsa ya ƙaru su ma samun duka waɗancan zai ƙaru."

Idan aka yi hakan, a cewarsa, walwalar al'umma za ta ƙaru saboda Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasar da ta fi yawan mutanen da ke dogaro a kan wasu.

"Ma'aikatan nan suna da iyalai da suke kula da su. Idan aka ƙara albashin zai ba su damar ƙara kula da iyalan nasu da kuma mutanen da suka dogara da su."

Shi ma Dr Murtala Abdullahi Kwarah na jami'ar ta Umaru Musa 'Yar'adua ya yarda wannan batu, yana mai cewa "ƙarin albashi a Najeriya ya zama wajibi".

"Ƙarin albashin nan, idan ba a yi shi ba babu abin da za a iya yi. Gara ma a ƙara musu ta yadda idan an samu hauhawar farashin suna da abin da za su iya saya," a cewarsa.

'Idan ba a ɗauki wasu matakai ba ƙarin albashin ba shi da amfani'

Harwayau, Dr Murtala Abdullahi Kwarah na Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua na ganin wannan ƙarin albashi ba zai yi wani amfani ba har sai gwamnati ta ɗauki wasu matakai game da tattalin arziki.

"Na farko dai wannan kaikomo da muke fama da shi na [darajar] dalar Amurka, ya kamata a ce gwamnati ta samu daidaito," in ji masanin tattalin arzikin.

Shi ma Dr Abdussalam ya amince da wannan batu, yana mai cewa dole ne sai an duba sauran buƙatun ma'aikaci ba wai a ba shi tsabar kuɗi kawai ba.

"Akwai sauran abubuwan da ma'aikaci ke buƙata kamar sufurin zuwa wajen aiki, da kiwon lafiyarsa, waɗanda suke buƙatar a samar da masu sauƙi tukunna.

"Misali, duk yawan albashin mutum a Najeriya zai yi wuya ya iya sayen fili har ma ya gina gida. Ko kuma wata rana rashin lafiya ta fi ƙarfin albashin mutum. Maimakon a bai wa ma'aikaci kuɗi ya tafi kasuwa ya yi ta fama da farashi, gara a sama masa waɗannan abubuwan cikin sauƙi idan ya so shi kuma ya sayi sauran abubuwa da kuɗin nasa."

Ta inda ƙarin albashin ba zai yi amfani ba

Duk da irin zaƙuwa da ma'aikata ke nunawa wajen fara karɓar sabon albashin, idan aka kalli ƙarin ta wasu hanyoyi za a hango rashin amfaninsa.

Mafi girma daga ciki shi ne janyo hauhawar farashi.

"A sabgar albashi akwai abin da ake kira "cost of production" ko kuma kuɗin da ake kashewa wajen samar da kayayyaki. Idan aka ƙara wa ma'aikata albashi hakan na nufin kuɗin da gwamnati ko kamfanoni ke kashewa ya ƙaru," kamar yadda Dr Abdussalam ya bayyana.

"To akwai yiwuwar wannan ƙarin ya jawo ƙaruwar farashin kaya ko yaya ne."

Ya ƙara da cewa "idan kuɗin da ke zagayawa a hannun mutane suka ƙaru shi ma zai iya jawo tashin farashi".