Ƙwazon da Arsenal ta yi a Premier tun da aka shiga 2024

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta sa ƙwazo a bana da ta kai tana mataki na daya a kan teburin Premier League da maki 86 da tazarar maki daya tsakani da Manchester City ta biyu.

Ranar Lahadi Gunners ta koma jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Ingila, bayan da ta je ta ci Manchester United 1-0 a Old Trafford.

Tun a ranar Asabar City ta je ta ci Fulham, inda hakan ya sa ta hau kan teburin gasar, wadda za ta buga kwantan wasa da Tottenham ranar Talata.

Arsenal na fatan lashe Premier League na bana, kuma da gaske take a bana tun da aka fara kakar nan.

Sai dai kungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama ta kara sa kaimi tun daga lokacin da aka shiga sabuwar shekara ta 2024.

Jerin kwazon da Arsenal ta yi a 2024:

Arsenal ta lashe wasa 15 da canjaras da Manchester City da rashin nasara a hannun Aston Villa a 2024 da cin kwallo 52 aka zura mata shida a raga daga sabuwar shekarar.

Haka kuma Gunners ta yi wasa 11 a waje ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba a Premier a bana, Chelsea ce mai tarihin 12 a 2008/09.

Gunners ta yi nasarar cin wasa 27 a bana a Premier League, kakar da tafi yin kwazo ita ce 1970/71 da ta ci fafatawa 29.

Haka kuma Gunners ta ci kwallo 89 a Premier - kakar da ta zura kwallaye da yawa tun bayan 1963/64 da ta ci 90.

Nasarar da Arsenal ta yi a Old Trafford ranar Lahadi ya sa ta doke United gida da waje a kakar nan, karon farko tun bayan Satumbar 1998.

Karo na hudu da Gunners ta doke United gida da waje idan aka hada da 1997-98 da 2001-02 da kuma 2006-07.