Da kyar idan Carvajal zai yi wa Sifaniya wasa da Costa Rica

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Watakila Dani Cavajal ba zai yi tawagar Sifaniya wasan farko da za ta fara a Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar ba.
Ranar Laraba Sifaniya za ta kara da Costa Rica a wasan farko a rukuni na biyar da ya hada da Jamus da kuma Japan.
Mai shekara 30, bai yi atisaye cikin 'yan wasan tawagar Sifaniya ba a filin motsa jiki da ke jami'ar Doha ba, sakamakon rashin lafiya.
Sifaniya za ta maye gurbinsa da Cesar Azpilicueta.
Sai dai Morata ya fara kar bar horo, wanda ya yi zazzabi kamar Carvahal hadi da ciwon ciki.
Sifaniya, wadda ta lashe kofin duniya a 2010 a Afirka ta Kudu, za ta buga wasa na biyu mai zafi a cikin rukuni da Jamus, sannan ta karkare da Japan.







