Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Champions League: Wa zai kai zagayen gaba Atletico Inter PSV ko Dortmund?
Za a buga wasa na biyu a Champions League zagayen 'yan 16 tsakanin Atletico Madrid da Inter Milan ranar Laraba a Civitas Metropolitano de Madrid.
A wasan farko da suka kara a Italiya, Inter ce ta ci 1-0 ta hannun Marko Arnautovic
'Jerin wasa tsakanin Atletico da Inter Milan
2023/2024
Champions League Talata 20 ga watan Fabrairun 2024
- Inter 1 - 0 Atl Madrid
2010/2011
European Super Cup Juma'a 27 ga watan Agustan 2010
- Inter 0 - 2 Atl Madrid
A wasan farko tsakanin kungiyoyin biyu an yi zaton cewar Marcus Thuram da Lautaro Martínez sune za su bai wa Atlético de Madrid ciwon kai a Italiya.
To sai dai Marko Arnautović ne ya ci wa Inter kwallon - tsohon dan wasan Stoke City da West Ham ya shiga wasan daga baya ya kuma ci kwallon saura minti 11 a tashi.
Sai dai Arnautovic ba zai buga karawar Laraba ba, sakamakon jinya, kenan za a sa ran Thuram da Martínez za su taka rawar gani da Inter ke bukata.
Daya wasan za a buga ne tsakanin Borussia Dortmund da PSV Eindhoven, wadanda suka tashi 1-1 a wasan farko.
Sun fara wasa a bana ranar 20 ga watan Fabrairun 2024, inda Luuk de Jong ya ci wa PSV Eindhoven kwallo a bugun fenariti, yayin da Donyell Malen ya ci wa Borussia Dortmund kwallo.
Wasa tsakanin Borussia Dortmunda da PSV Eindhoven
2023/2024
Champions League Talata 20 ga watan Fabrairun 2024
- PSV Eindhoven 1 - 1 B Dortmund
2002/2003
Champions League Talata 22 ga watan Oktoban 2002
- B Dortmund 1 - 1 PSV Eindhoven
Champions League Laraba 2 ga watan Oktoban 2002
- PSV Eindhoven 1 - 3 B Dortmund
Donyell Malen ne ya fara ci wa Dortmund kwallo a Eindhoven, kuma dan kasar Netherlands bai yi murnar kwallon da ya zura a raga ba.
Ya koma taka leda zuwa Jamus a 2021.
Daga baya PSV ta farke ta hannun Luuk de Jog a bugun daga kai sai mai tsaron raga, kuma na 28 da ya zura a raga a kakar nan.