Chelsea ta dauki Koulibaly daga Napoli

Koulibaly

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Chelsea ta dauki dan wasan bayan Napoli, Kalidou Koulibaly kan kwantiragin kaka hudu daga kungiyar da ke buga Serie A.

Dan kwallon mai shekara 31, dan asalin kasar Senegal, ya koma Napoli daga Genk a 2014, wadda ya yi wa wasa 317.

Zuwansa Stamford Bridge ya biyo bayan tafiyar 'yan wasan baya na Chelsea Antonio Rudiger zuwa Real Madrid da kuma Christensen da Barcelona da dauke shi, bayan karewar yarjejeniyarsu a kakar da ta wuce.

"Ina cikin farin ciki zuwa na Chelsea," in ji Koulibaly.

"Babbar kungiya ce a duniya, kuma mafarkina a kullum shi ne na buga wasa a gasar Firimiya.

Tun a 2016 Chelsea ta nemi ta saye ni, amma bamu daidaita ba.

"Bayan na yi magana da abokai na da suka hada da Edou Mendy da Jorginho, sun karfafamin gwiwar da na koma Stamford Bridge.''

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Koulibaly ya fara buga wa babbar tawagar Senegal tamaula a Satumban 2015, tun daga nan ya yi wasa 62, ya jagoranci kasar a matsayin kaftin a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2022.

Shi ne dan wasa na biyu da Chelsea ta sayo a kakar nan, bayan Raheem Sterling daga Manchester City kan fam miliyan 50 , tun bayan da wasu attajirai suka mallaki kungiyar karkashin jagorancin Todd Boehly, bayan da sakawa Roman Abramovich takunkumi..

Boehly ya ce: " Koulibaly na cikin 'yan wasa masu tsaron baya da suka shahara a duniya, kwarewarsa za ta taimaka mana sosai, muna farin ciki da zuwansa Chelsea''.