Manchester United za ta farfaɗo - Ten Hag

Asalin hoton, Getty Images
Erik ten Hag ya ce ya shaida wa 'yan wasansa na Manchester United cewa kakar wasan bana "za ta yi mana kyau".
United tana matsayi na ƙarshe a rukuninta na gasar zakarun Turai bayan ta sha kashi a hannun FC Copenhagen kuma tana matsayi na takwas a teburin Premier.
Dukan da United ta sha a hannun Copenhagen da ci 4-3 ya janyo ce-ce-ku-ce, musamman saboda jan kati da aka nuna wa Marcus Rashford lokacin da Red Devils ke ci 2-0.
Rashford ya taka ƙafar Elias Jelert, lamarin da ya sa aka tura alƙalin wasa Donatas Rumsas zuwa wajen duba alƙalin wasa na bidiyo da ke gefen filin wasa, kuma daga nan ya bai wa Rashford jan kati.
"Na ji takaici matuka game da irin wannan hukunci, ina ganin bai kamata a ce wasan ya kasance haka ba, in ji Ten Hag.
Ya kuma ƙara da cewa "Za mu ci gaba da gwagwarmaya saboda ina da tabbacin cewa 'yan wasan na sa'ar mu za ta sauya - a lokaci guda a kakar wasan nan za ta yi mana kyau."
A wasanta na gaba United za ta fafata da Luton Town ranar Asabar mai zuwa a gasar Premier.








