Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Makabartar da aka binne 'yan Gaza da aka kashe a yaƙin duniya sama da shekara 100
Fararen duwatsu, ciyayi da kuma iyakoki na furanni sune suka kayata manyan makabartun yaƙi na arewacin Faransa da Belgium.
Sai dai, wannan wuri da ake binne sojojin da aka kashe a yaƙin duniya na biyu yana a zirin Gaza.
Makabartar ta zama wani wuri mai koren da ba a saba gani ba a cikin yankin mai cunkoson jama'a, wajen da rikicin Isra'ila da Falasdinu ya yi kamari.
Sadaukarwa da ƙwarewar ƙananan ƙungiyar ma'aikatan cikin gida a bayyane yake.
Abin sha'awar shi ne duk sun fito ne daga iyalai waɗanda aka ba da wannan aikin tun magabata da suka wuce.
"Ina jin ni ɗan wannan makabarta ne," in ji Ibrahim Jaradah, shugaban masu kula da makabarta a yanzu na hukumar kula da kaburbura ta Commonwealth , wanda tuna shekaru 100 daidai da kakansa ya fara yin irin wannan aiki.
A yanzu yana da shekara 32, an haife shi a cikin gidan da har yanzu yake zaune a ciki kuma a wurin ya girma tsakanin kukan tsuntsaye da kuma filfilo.
“Lokacin da nake karami burina shi ne in yi aiki a nan,” in ji Ibrahim, yana bayyana yadda yake taimaka wa mahaifinsa da ayyukan ofis da shuka iri da yin takin zamani. "Na koya daga iyalanmu na son aikinmu."
"Muna jin yana da matukar muhimmanci. Waɗannan mutane sun ba da rayukansu don kasashensu, an bamu amanar kula da wannan wuri mai tarihi."
Makabartar yaki na zirin Gaza na ɗaya daga cikin wurare biyu mallakin CWGC a wannan karamin yankin Falasdinu.
Tana da kaburburan mutum 3,691- wanda ya kunshi 'yan birtaniya 3082 da 'yan Indiya 50 da 'yan Poland 36 da 'yan Kanada 23 da 'yan New Zealand 23 da sauran mutane daga Kudancin Afirka da Girka da Masar da Jamus da Faransa da kuma 'yan Yugoslavia.
An binne yawancin mutane da ke makabartar ne a lokacin yaƙin duniya na ɗaya, inda da dama daga ciki suka kasance maza 'yan shekara 20 zuwa 30.
A shekarar 1917, Gaza ta gamu da yaƙe-yaƙe guda uku tsakanin dakarun Masar - da Birtaniya ta kafa - da kuma sojojin daular Ottoman, har sai da suka kwace iko da birnin.
A cikin makabartar, an rubuta sunayen sojojin da suka kwanta dama da muƙamansu da rundunonisu da shekarunsu da kuma ranar da suka mutu.
Akwai Kiristoci da Yahudawa da Musulmai da kuma 'yan Hindu, inda aka binne kowanne da waɗanda addininsu ɗaya.
"Idan muka sunaye daban-daban, za mu so mu san su waye ne waɗannan mutane, su waye iyalansu? Me suke yi a rayuwarsu?" in ji Ibrahim wanda ke tuna abubuwa lokacin da muke zagayawa kabari bayan kabari.
Gyara da sake gina makabarta
Kakan Ibrahim na biyu, Rabie Jaradah, ya fara aiki a makabartar da hukumar kula da makabartu ta ƙasashen Commonwealth ke kula da shi a Beersheba a shekarar 1923.
Iyalansa sun zama 'yan gudun hijira lokacin yaƙin wanda ya biyo baya da kirkirar jihar Isra'ila a 1948. Sun tsere zuwa Gaza, inda nan take aka ba shi umarnin kula da makabartun.
Ɗa ga Rabie, wanda ake kira Ibrahim, shi ma ya kawo ɗansa daga bisani mai suna Essam, don taimaka masa lokacin da yake zuwa makaranta.
Tsauraran matakai da Isra'ila da Masar suka saka a kan iyakoki a lokuta da dama, ya janyo wahala ga 'yan ƙasashen waje da ke son kai ziyara - ban da jami'an diflomasiyya da 'yan aikin agaji da kuma 'yan jarida - don ziyara zuwa yankunan Falasɗinawa.
Ina buƙatar katin 'yan jarida na Isra'ila da kuma dama daga kungiyar Hamas da ke mulki a Zirin Gaza domin shiga yankin.
Sai dai, Essam Jiddah, wanda ya yi ritaya, yana tuna abubuwa da suka faru a lokuta da dama.
"Babu wata barazana a nan, mun kasance muna samun baki da yawa. Muna zama da su ko zagayawa da su, rayuwa tana da daɗi,'' in ji shi.
"Na kan gane yanayin da mutane suke ciki, haɗe da hawaye a idanunsu lokacin da suke kan kaburburan kakanninsu."
Tun bayan da Hamas ta kwace iko da Gaza a shekarar 2007, an yi ta samun artabu da bata-kashi da kuma faɗa tsakanin Falasɗinawa da 'yan Isra'ila.
Makamai masu linzami sun faɗa makabartar har sau uku. Akwai lokacin da aka lalata allunan kaburbura kusan guda 300, inda sai da ta kai aka sake maye gurbinsu da wasu.
An sake datsa alluna da furanni bayan wani kazamin rikicin da ya hana ma'aikatan wurin zuwa aiki.
"Duk lokacin da muka dawo aiki, muna mayar da abubuwa yadda suke a baya,'' in ji Ibrahim.
"Muna aiki cikin yanayi na ƙalubale iri iri."
Wannan ya haɗa da ƙarancin wutar lantarki a kullu yaumin a Zirin Gaza da rashin ruwa da takunkumai kan shigo da kayayyaki waɗanda suka sanya ake wahala wajen tayar da injuna don ba da hasken wuta da kuma na yanka ciyayi.
Ibrahim ya ce shi da ma'aikatansa sun koyi sanin muhimmancin abubuwa da kuma ilimin 'yan uwansu.
Na haɗu da Mohammed Atalah, mai shekara 23, yana yanke ciyayi tsakanin kaburbura, abu da mahaifinsa da kuma kakansa suka yi su ma."
"Ina son aikin,'' in ji shi. "Idan na fita da safe, ina samun karfin jiki wajen kallon wannan wuri mai launin kore. Ina ji abun girmamawa ne yin aiki a nan."
Girmama waɗanda suka rasu
Mutane da dama ne ke kai ziyara makabartar. Iyaye mata da yaransu su kan je su zauna suna tattaunawa kusa da wani kabarin ɗan Indiya, inda wasu kuma ke tsayawa karkashin wata karamar bishiya mai furanni.
"Wurin yana da kyau sosai. Ina jin dadin zama a nan. Wurin yana da launin kore mai matukar kyau da kuma ke da tarihi," kamar yadda ɗaya daga cikinsu mai suna Karim ya faɗa mini.
Um Iyad, sanye da bakin nikabi, zuciyar ta na raya mata damuwa da za a iya fuskanta yayin da take tafiya cikin hankali tare da yarta.
"Muna cikin damuwa, sannan a cikin al-Qur'ani, an faɗa cewa idan kana cikin matsala, to ka ziyarci makabarta,'' in ji ta. "Na zo nan ne domin na huta."
Ibrahim bai cika tattaunawa mai yawa ba da waɗanda ke zuwa makabartar. A wasu lokuta yana zagayawa da 'yan makaranta da kuma masu bincike daga jami'o'i a makabartar.
"Yana da muhimmanci a mutunta dukkan waɗanda suka rasu ba tare da duba 'yan wace ƙasa ba da kuma inda suka fito. Idan mutanen Gaza basu girmama ko amincewa da makabartar ba, ba za ku ganta a haka ba,'' in ji Ibrahim.
Yana da yaƙinin cewa kowaye kuma ko daga ina ya fito, sun ɗauki babban darasi.
"Muna jin masu ƙananan shekaru da aka binne a nan ya shafi mutane,'' in ji Ibrahim.
"Muna fatan za su ga hakan a matsayin tasirin yaƙe-yaƙe sannan zaman lafiya shi ne abu mafi muhimmanci a duniya.''