Ranar tsaftar baki: Yadda ya kamata ku yi buroshi
An wallafa
A wannan bidiyon, BBC ta tattauna da Shamara Audu, wata likitar haƙora inda ta yi bayyani daki-daki kan hanyoyin da ya kamata mutane su bi wajen tsaftace haƙoransu.
Ta bayyana haka ne a wani ɓangare na bikin ranar tsaftar baki ta duniya da ake yi duk ranar 20 ga watan Maris ɗin kowace shekara.
Ɗaukar Bidiyo: Joseph Jegede.








