Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Poland na gab da zama ƙasa ta farko da za a fitar daga Euro 2024
Ƙwallayen da Christoph Baumgartner da Marko Arnautovic suka ci wa Austria sun bai wa ƙasar damar doke Poland a wasa na biyu na ciin rukunin gasar ƙasashen Turai ta Euro 2024.
Yayin da duka tawagogin suka yi rashin nasara a wasanninsu na farko na rukunin D a hannun Faransa da Netherlands, suna sane da cewa duk wanda aka ci zai koma gida daga gasar.
Austria ce ta fara ci lokacin da Gernot Trauner ya ci ƙwallo da ka bayan Phillipp Mwene ya bugo ta a sama.
Bayan minti 30 kuma Krzysztof Piatek ya farke ta, kafin daga baya Baumgartner ya ci biyu.
Idan har wasa tsakanin Faransa da Netherlands ya tashi kunnen doki to Poland ta fice daga gasar baki ɗaya.
Idan kuma wata ta yi nasara to tawagar ta ɗan wasan Barcelona Lewandowski na da damar fitowa amma dole sai ta ci wasanta na gaba da Faransa, sannan kuma ta yi fatan a doke Slovakia ko Netherlands a nasu wasan.