Arsenal ta yi kaka 21 ba tare da daukar Premier League ba

An wallafa

Arsenal ta kasa daukar Premier League na bana, duk da doke Everton 2-1 a wasan mako na 38 ranar Lahadi a Emirates.

Hakan ya biyo bayan da Manchester City ta yi nasara a kan West Ham United 3-1 a Etihad, kofi na hudu a jere na Premier da ta dauka a tarihi, babu mai wannan bajintar.

Saura minti biyar su je hutu ne Everton ta fara cin kwallo ta hannun Idrissa Gueye, sai dai minti uku tsakani Gunners ta farke ta hannun Takehiro Tomiyasu.

Daf da za a tashi wasan ne Arsenal ta kara na biyu ta hannun Kai Havertz, hakan ya sa ta hada maki ukun da take bukata.

Gunners ta ci wasan karshe a Premier League a kowacce kaka 13 kenan da ta gabata.

Arsenal ta kare a mataki na biyu a teburi da 89 da tazarar biyu tsakani da Manchester City, wadda ta dauki kofin.

Gunners din ta ci wasa 28 a bana, irin yawan wadanda City ta ci da canjaras biyar da rashin nasara biyar da cin kwallo 91 aka zura mata 29 a raga.

Tuni Arsenal ta kafa tarihin cin wasa 28 a kakar tamaula ta bana, wadda ta taba lashe karawa 29 a 1970/71 da cin wasa 28 a 1930/31.

Arsenal ta yi karawa 18 a Premier ta bana ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba, kaka mafi kwazo da ta yi hakan tun bayan 1998/99.

William Saliba ya buga wa Arsenal dukkan wasannin Premier na kakar nan, kamar yadda Max Kilman na Wolverhampton ya yi.

Wannan ita ce kaka ta 21 rabonda Gunners ta dauki Premier League tun 2003/04 karkashin Arsene Wenger.

Wannan shi ne karo na biyu a jere tana karewa a mataki na biyun teburi, bayan da a bara ma City ta lashe kofin.

Rabonda Arsenal ta dauki wani kofi tun FA Cup da ta lashe na 14 jimilla a 2019/20, ba wadda ta kaita wannan bajintar.

Haka kuma a 2023 ta yi nasarar daukar Community Shield, wanda ake yi mabudin fara Premier League.