Ayatollah Ali Khamenei ya jagoranci sallar jana'izar tsohon shugaban Iran

An wallafa

Jagoran addinin ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ne ya jagoranci sallar da aka yi wa marigayi tsohon shugaban ƙasar Ebrahim Raisi da ministan ƙasashen wajen ƙasar da sauran mutum shida dasuka rasu ranar Lahadi sakamakon hatsarin jirgi mai saukar ungulu.

Ayatollah Khamenei ya jagoranci sallar ne a farfarjiyar jami'ar Tehran inda aka jera gawarwakin mamatan da aka naɗe da tutocin ƙasar ta Iran.

“Ya Allah, ba mu san komai a gare shi ba sai alkairi," in ji Khamenei a lokacin da yake yi masa addu'ar mamaci da harshen Larabci.

Shugaban riƙon ƙwarya Mohammad Mokhber yana tsaye kusa da jagoran addinin yana mai shasheka a bayyane lokacin sallar

Daga nan ne kuma al'umma suka ɗauki makarar a kafaɗunsu inda suke rera wakokin "mutuwa ga Amurka."

Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron jana'izar sun haɗa da shugaban ƙungiyar Hamas, Isma'il Haniyeh.

Haniyeh ya bayyana maragayi Ebrahim Raisi da “ na zo nan a madadin al'ummar Falasɗinawa, a madadin masu jajircewa na Gaza.....domin nuna alhinimu".

Yau dai ranar hutu ce a Iran, kuma ɗaya daga cikin ranaku biyar na zaman makokin rashin tsohon shugaban da wasu jami’ai bakwai.

Za a zagaya da gawarwakin mutanen takwas a sassan birnin, cikin akwatunan da aka yi wa kwalliya da tutar Iran, daga baya kuma a ajiye su a dandalin Azadi inda a baya marigayi Ebraihim Raisi yake gabatar da jawabi ga al'ummar ƙasar.

Kamar dai yadda aka yi ranar Talata, a ranar Laraba ma ana sa ran dubun dubatan masu alhini sun yi jerin gwano a kan titunan birnin har zuwa dandalin Azadi.

Zagayen na bankwana da gawar tsohon shugaban ya ɗauki wani salo na siyasa, inda masu ra’ayin riƙau da ke mulkin ƙasar ke fatan yin amfani da lokacin wajen nuna haɗin kai da neman goyon bayan jama’a.

Ana kuma yaɗa hotuna da bidiyon abubuwan da ke faruwa a sassan ƙasar, musamman a shafukan sada zumunta, yayin da yan sanda ke gargadi a kan yada labaran karya da na cin mutumci.