Barcelona za ta bayar da aron Torres

An wallafa

Ƙungiyar Barcelona na duba yiwuwar bayar da aro dan wasanta ba gefe, Ferran Torres.

Torres ya koma Barcelona daga Manchester City a farkon shekara ta 2022.

Duk da cewa kulob din na fuskantar matsalar karancin kudi, shugaban kungiyar Joan Laporta ya amince da yarjejeniyar da ta kai kusab fam miliyan 50.

Amma yanzu rahotanni na cewa za a nemi ba da aron Torres zuwa wata ƙungiya a kakar wasa mai zuwa saboda ya samu buga wasanni don kada farashin sa ya faɗi.

Ya samu kansa a halin rashin samun wuri a Barcelona sakamakon canjin tsarin da kocin ya yi, kuma ana ganin cewa idan aka cigaba a haka dan wasan ba zai yi kasuwa ba idan aka tashi sayar da shi.

Haka kuma bayar da aron Torres zai taimakawa Barcelona wurin rage kudaden da ta ke kashewa kan albashi idan har ta sami ƙungiyar da za ta karɓe shi.