Lokuta biyar da mutanen gari suka yi wa jami'an tsaro kisan gilla a Najeriya

Asalin hoton, X/Nigerian Army
- Marubuci, Usman Minjibir
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa, Abuja
- An wallafa
Idan ka cire kisan da kungiyoyin 'ta'addanci' kamar Boko Haram da ƴan awaren Biafra da ƴan bindiga masu satar jama'a ke yi, wani kisan da ke ci wa jami'an tsaron Najeriya tuwo a ƙwarya shi ne wanda al'umma kan yi wa jami'an.
Akan samu yanayin da jami'an tsaro kan je gari domin kwantar da tarzoma amma kuma sai reshe ya juye da mujiya, inda ƴan garin kan yi musu kisa irin na a-tara-a-tara, wani abu da a wasu lokutan bayan ake zargin ya janyo ɗaukar mummunar fansa daga jami'an tsaron.
A lokuta daban-daban a Najeriya, jami'an tsaron musamman sojoji ko ƴansanda kan far wa irin waɗannan garuruwa inda suke ɗaukar matakin ramuwar gayya ba tare da banbance babba da yaro ko namiji da mace ba.
A mafi yawancin lokaci, matasa masu jini a jika ne kan aikata irin wannan aika-aika kan jami'an tsaron amma kuma sai su gudu su bar ƴan'uwansu, waɗanda daga ƙarshe su ne za su fuskanci fushin jami'an tsaron.
Yanzu haka dai sojojin Najeriya na alhinin rashin ƴan'uwansu guda 17 da wasu matasa suka kashe a jihar Delta, ranar Alhamis.
Kuma wannan shi ne jerin kisan gilla na biyar ga jami'an tsaro a Najeriya daga shekarar 1999 lokacin da Najeriya ta koma mulkin farar hula zuwa yanzu.
Ga jerin garuruwa biyar da al'umma suka yi wa jami'an tsaro kisan-gilla.

Asalin hoton, Getty Images
Odi na jihar Bayelsa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A watan Nuwamban shekarar 1999 ne wani gungun matasa a kusa da garin Odi da ke kamar hukumar Kolokuma/Opokuma a jihar Bayelsa a yankin Neja Delta, ya ƙaddamar da wani nau'in kisan gilla ga sojoji da ƴansandan Najeriya guda 12, a kan hanyarsu ta zuwa garin domin kwantar da wata tarzoma.
To sai dai a wani hari mai kama da na ramuwar gayya, sojojin sun far wa garin na Odi inda suka ƙaddamar da hari irin na kan-mai-uwa-da-wabi.
Hukumomi da ƙungiyoyin masu rajin kare hakkin ɗan'adam a lokacin sun ce an kashe farar hula kimanin 900.
Sai dai hukumomin sojoji sun musanta zarge-zargen, inda suka ce sun yi ƙoƙarin tsamo ɓata garin da suka aikata kisan gillar ne.
A shekarar 2013 ne kuma wata babbar kotu a Abuja ta umarci gwamnatin Najeriya ta biya al'ummar Odi diyyar kuɗi har naira biliyan 37.6 na mutanen da aka kashe.
To sai dai gwamnatin lokacin ta Goodluck Jonathan ta biya naira biliyan 15, bayan cimma warware matsalar da shugabannin al'ummar garin.
Zaki-Biam na jihar Benue
Su ma matasan garin Zaki-Biam da ke jihar Benue sun yi wa sojoji kwantan-ɓauna inda suka kashe guda 19 a watan Oktoban 2001.
Gwamnati ce dai ta aika da rundunar sojin domin kwantar da tarzoma tsakanin kabilar Tivi da Jukun da suke faɗa da juna a ƙananan hukumomin Zaki-Biam da ke Benue da Logo da ke jihar Taraba.
Kisan sojojin ya janyo rundunar soji ta far wa garin na Zaki-Biam domin abin da suka kira zaƙulo waɗanda suka aikata laifin da kuma ɗaukar fansa.
Ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Human Rights Watch ta ce sojojin Najeriya sun kashe ɗaruruwan mutane da ƙona muhalli. Sojojin dai sun musanta zarge-zargen.
Alakyo na jihar Nassarawa
A shekarar 2013 ne wani mutum da ake zargin matsafi ne mai suna Baba Alakyo a ƙauyen Alakyo na jihar Nassarawa ya yi sanadiyyar mutuwar ƴansanda fiye da guda 55 da jami'an tsaron farin kaya fiye da 10.
Rahotanni dai sun ce wasu matasa ne mabiya matsafin da ake kira 'Ombatse' suka yi ta kai wa jami'an tsaron hare-hare a ƙoƙarin jami'an na daƙile ayyukan tsafin da Baba Alakyo ke yi da ke salwantar da rayukan al'umma.
Bayanai sun tabbatar da cewa ƴan ƙungiyar asirin sun yi wa jami'an tsaron da aka aika daga Abuja, kwanton-ɓauna inda suka ƙwace makamansu sannan suka yi musu kisan gilla kafin daga bisani su ƙona gawarwakinsu.
Wani babban ɗansanda wanda ya shaida faruwar al'amarin a lokacin ya faɗa wa manema labarai cewa "wannan ne yanayin da na taɓa ganin an kashe jami'an tsaro a ruwan sanyi a tsawon shekaru 30 da na yi ina aikin tsaro."
Dura-Du na jihar Filato
Dura wani ƙauye ne da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.
Sojoji sun zargi matasan garin da kisan wani janar din soja mai suna Janar Idris Alƙali wanda aka neme shi tare da motarsa aka rasa a 2018.
Janar Alkali dai na tafiya ne a mota daga Abuja zuwa Bauchi a ranar 30 ga watan Agustan 2018.
To sai dai daga bisani an tsinci gawar janar ɗin a wani kududdufin ruwa bayan yi masa kisan gilla.
Janar ɗin dai na kan hanyarsa ta zuwa Bauchi inda ya yi arangama da wasu matasa masu zanga-zanga da ke nuna fushinsu kan kisan mutanensu 11 da suke zargi wasu da suka kai musu hari sun yi.
Okuama na jihar Delta

Asalin hoton, NA/TWITTER
Gari ne da ke ƙarƙashin jihar Delta a yankin Neja Delta, inda wasu matasa suka mamayi sojojin da ke kwantar da tarzoma a yankin har ma suka kashe guda 17 ranar 14 ga watan Maris, 2024.
Rahotanni sun ce matasan sun yi wa sojojin kisan wulaƙanci, inda suka yi wa gawarwakinsu gunduwa-gunduwa bayan sun kashe su.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu dai ya bayar da umarnin a nemo waɗanda suka aikata kisan gillar a duk inda suke.
Rahotanni sun nuna cewa al'ummar garin Okuama sun tsere sakamakon zaman ɗarɗar da fargabar abin da ka iya zuwa ya komo.
Me hare-haren ke nufi?
Masanin harkar tsaro kuma shugaban kamfanin da ke samar da bayanai dangane da tsaro na Beacon Consulting, Malam Kabiru Adamu ya lissafa wasu dalilai da ke janyo irin waɗannan hare-hare kan jami'an tsaro:
- Akwai rashin kyakkyawar alaƙa tsakanin jami'an tsaro da al'ummar da suke bai wa tsaro walau dai rashin sanin yankin ko ala'ada ko addinin mutanen yankin da suke karewa.
- Ɓangarorin al'ummu masu rikici da juna kan zargi jami'an tsaro da goyon bayan wani ɓangare yayin kwantar da tarzoma.
- Wani lokacin kuma idan jami'an tsaron suka ƙi bai wa wani ɓangare goyon baya ko kuma makamai to sai ɓangaren ya nemi ya ga bayan su bisa zargin su ma abokan faɗa ne.
- Hari kan jami'an tsaro na nuni da irin illar yawaitar makamai a hannun farar hula domin a duk lokacin da mutane ke ɗauke da makamai suna jin daidai suke da kowane jami'in tsaro.
Mafita
Malam kabiru Adamu ya ce gwamnati da jami'an tsaro da ɗaukacin al'umma na da rawar da za su taka wajen kawo ƙarshen kashe jami'an tsaro waɗanda su ne ƙashin bayan tsaron kowace al'umma. Ya kuma zayyana waɗannan nan matakai kamar haka:
- Dole ne a hukunta duk wanda aka samu da laifin kisan jama'in tsaro domin ya zamo izna ga masu sha'awar yin hakan a nan gaba.
- Dole ne a sauya tsarin tsaron kasa
- Dole ne a samar wa jami'an tsaro kayan aikin da suka dace
- Dole ne su jami'an tsaro su rinka tattara bayanan sirri kafin gudanar da ayyukan.
- Dole ne a saka kaunar jami'an tsaro a zukatan ƴan ƙasa domin su san irin muhimmancin da suke da su ga rayuwarsu da ta kasar baki daya.
- Dole ne a rinka sanin wane jami'in tsaro ne ya dace da yanayi - misali shin dan sanda ne ya dace ko kuma soja. "Ya kamata a rinka aunawa a gani ba kawai kowane rikici a kai soja ba ko kuma dan sanda." In ji Malam Kabiru.
Da ma dai Nigeria dai ta yi rashin dubban jami'an tsaro a tsawon shekaru 20 sakamakon rikice-rikicen da kasar ta yi fama da su.
Bayanai daga masana tsaro ya nuna yadda Najeriyar ta rasa jami'an tsaro fiye da 2000 a tsawon shekaru 10 da suka gabata. Wata kididdiga a 2021 ta nuna Najeriya na da jami'an tsaro kasa da 500,000 da masana kan ce sun yi wa kasar mai yawan al'umma fiye da miliyan biyu kadan.







