Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ra'ayi Riga: Kan matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya 15/03/2025
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1
A shirinmu na Ra'ayi Riga wannan makon, mun nazari ne kan batun yara waɗanda ba sa zuwa makaranta a Najeriya.
A kwanakin baya ne dai asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya sake nanata cewa akwai adadin yara masu yawan gaske waɗanda ba sa zuwa makaranta a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Shin me yake kawo wannan matsalar?
Wane mataki gwamnatin take ɗauka?
Shin laifin waye?
Me ya kamata a yi?
Waɗannan na daga cikin batutuwan da muka tattauna a cikin shirin namu na Ra'ayi Riga na wannan makon.