Lookman ba zai buga wa Atalanta wasa da Barcelona ba

Asalin hoton, Getty Images
Ademola Lookman ba zai buga wa Atalanta Champions League da za ta kara da Barcelona ba, kamar yadda ƙungiyar da ke buga Serie A ta sanar ranar Talata.
Ɗan wasan tawagar Najeriya ya ji rauni a gwiwa a lokacin da yake atisaye tare da sauran ƴan wasan ƙungiyar.
Ƙungiyar ta Italiya ta sanar cewar Lookman zai yi jinyar mako uku, kuma hakan koma baya ne, bayan da ya ci ƙwallo 14 a bana ya bayar da shida aka zura a raga.
Shi ne wanda ya ci ƙwallo uku rigis a bara a wasan karshe a Europa League kan Bayern Leverkusen, mai rike da Bundesliga a lokacin.
Ƙungiyar da Gian Piero Gasperini ke jan ragama tana cikin masu fatan lashe Serie A na kakar nan, tana da tazarar maki bakwai tsakani da Napoli ta ɗaya.
Haka kuma Atalanta tana kokari a wasannin da take yi a babbar gasar zakarun Turai ta kakar nan, wadda aka sauya wa fasali.
Atalanta tana da maki 14 a mataki na bakwai a teburin Champions League, bayan cin wasa huɗu da canjaras biyu aka doke ta karawa ɗaya.
Barcelona ce ta biyun teburin gasar zakarun Turai na bana da maki 18, bayan nasara shida da rashin nasara a wasa ɗaya.
Wasannin da za a buga ranar Laraba a Champions League.
- Aston Villa da Celtic
- Barcelona da Atalanta
- Bayer Leverkusen da Sparta Prague
- Bayern Munich da Slovan Bratislava
- Borussia Dortmund da Shakhtar Donetsk
- Brest da Real Madrid
- Dinamo Zagreb da AC Milan
- Girona da Arsenal
- Inter Milan da Monaco
- Juventus da Benfica
- Lille da Feyenoord
- Manchester City da Club Brugge
- PSV da Liverpool
- Red Bull Salzburg da Atlético Madrid
- Sporting da Bologna
- Sturm Graz da RB Leipzig
- Stuttgart da PSG
- Young Boys da Red Star Belgrade











