Salah ya ci ƙwallo 25 a Premier 30 a dukkan karawa kawo yanzu

Asalin hoton, Getty Images
Kawo yanzu Mohamed Salah ya ci ƙwallo 25 a Premier League ya zura 30 a raga jimilla a dukkan karawa a Liverpool a bana.
Ranar Lahadi Liverpool ta doke Manchester City a wasan Premier a Etihad, Arne Slot ya yi nasara a kan Pep Guardiola gida da waje - ranar 1 ga watan Disamba Liverpool ta ci 2-0 a Anfield.
Salah na kan gaba a takarar ƙyautar takalmin zinare a cin ƙwallaye a Premier da tazarar shida tsakani da Erling Haaland, wanda bai buga wasan ranar Lahadi ba.
Ɗan wasan Newcastle United Alexander Isak, wanda ya ci Nottingham Forest biyu ranar Lahadi yana da ƙwallo 19 jimilla bayan kammala wasannin mako na 26.
Ɗan kasar Masar ya ci ƙwallo a cikin wasa 21 daga 27 a lik a kakar nan, inda Liverpool ta yi nasara 16 da canjaras biyar.
Haka kuma shi ne kan gaba a yawan bayar da ƙwallo a zura a raga mai 16 da tazarar shida tsakani da mai biye da shi.
Salah ya zama na farko a Premier da ya ci ƙwallo ko ya bayar aka zura a raga guda 40 ko fiye da haka a kaka ɗaya, wanda a bana ya ci 25 ya bayar da 16 aka zura a raga.
A kakar 2017/18 ya yi sanadin 42, wanda ya ci 32 ya kuma bayar da 10 aka zura a raga.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ci ƙwallo uku a Champions League da bayar da huɗu aka zura a raga da cin biyu da bayar da ɗaya aka zura a raga a Carabao Cup, jimilla yana da hannun a cin 51 a dukkan fafatawa kawo yanzu.
Salah yana ƙwazon nan duk da cewar ba a kai ga cimma yarjejeniya ba kan batun tsawaita zamansa a Liverpool.
Ɗan kasar Masar shi ne na uku a yawan cin ƙwallaye a Liverpool a tarihi, yayi kan-kan-kan a mataki na uku da Gordon Hodgson mai 241 a dukkan karawa.
Salah ya buga wasa 387 a Liverpool, shi kuwa Hodgson karawa 377 ya yi.
Ian Rush ne kan gaba da ƙwallo 346 a Liverpool, sai kuma Roger Hunt mai 285 a raga a mataki na biyu a cin ƙwallaye a tarihi a ƙungiyar Anfield.
Salah shi ne na shida a jerin zura ƙwallaye mai 182 a Premier, sauran ƙwallo biyu tsakaninsa da tarihin Sergio Aguero da Andy Cole mai 187 a raga.
Salah na mataki na 10 a jerin waɗan da suka bayar da ƙwallo aka zura a raga a Premier mai 85.
Ya lashe takalmin zinare a kakar farko da cin 32 a Liverpool a 2017/18,
Kawo yanzu Sallah na fatan karɓar ƙyautar takalmin zinare karo na huɗu a Premier League, zai yi kan-kan-kan da Thierry Henry.
An raba musu takalmin zinare tare da Sadio Mane da ɗan wasan Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang a 2018-19.
An kara raba musu takalmin zinare tare da ɗan ƙwallon Tottenham, Son Heung-min a 2021-22.











