Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool na son Tchouameni, Man United na bibiyar Branthwaite
Liverpool na shirin kashe fam miliyan 50 domin dauko dan wasan tsakiya na Faransa mai taka leda a Real Madrid Aurelien Tchouameni mai shekara 24. (Fichajes - in Spanish)
Juventus ma na son matashin ɗan wasan gaba Jonathan David, sai dai su ma kungiyoyin Manchester United, Liverpool da Arsenal na son dan wasan na Canada. (Corriere dello Sport - in Italian)
Manchester United na son dan wasan baya na Everton Jarrad Branthwaite, inda kulub din ya ware fam miliyan 70 don cinikin dan wasan na Ingila mai shekara 22 a sabon kwantiragi. (Mail - subscription required)
Brighton da Bayer Leverkusen na daga cikin wadanda suka nuna sha'awa kan matashin dan wasan mai tsaron gida na Serbia da ke taka leda a Red Star Belgrade Strahinja Stojkovic. (Football Insider, external)
Arsenal sun tattauna da eja din dan wasan gaba na Sporting Geovany Quenda, mai shekara 17, wanda kumngiyoyin Manchester United,da Manchester City da Liverpool ke zawarcinsa. (Teamtalk)
Ana shirin rage albashin ɗan wasan gaban Poland, Robert Lewandowski, mai shekara 36, domin ya samu damar ci gaba da zama a Barcelona. Matakin da dan wasan ya dauka ya sanya Kulub din ya daina nuna sha'awar dauko dan wasan gaba na Ingila kuma mai taka leda a Manchester Erling Haaland, mai shekara 24. (Sport - in Spanish)
AC Milan a shirye ta ke ta rubanya kudi domin dauko dan wasan tsakiya na Netherland Tijjani Reijnders, mai shekara 26, to amma su ma kungiyoyin Manchester City da Tottenham na nuna sha'awar dauko dan wasan. (Calciomercato - in Italian)
Dan wasan tsakiya na Ingila Harry Maguire, 31, ba zai bar Manchester United a watan Junairu ba, ya kuma yi amanna zai samu sabon kwantiragi a kulub din. (TBR Football)
Paris St-Germain na zawarcin dauko dan wasan gaban Colombia da ke taka leda a Aston Villa Jhon Duran, mai shekara 20. (Fichajes - in Spanish)