Aurelien Tchouameni ya zama na hudu mafi tsada da Real Madrid ta saya

An wallafa

Real Madrid ta dauki Aurelien Tchouameni daga Monaco kan yarjeniyar kaka shida, shi ne na hudu a jerin 'yan wasan da ta dauka mafi tsada a tarihi.

Wasu rahotanni na cewar Real Madrid ta sayo dan kwallon kan fam miliyan 68.3 da karin tsarabe-tsaraben da zai kai fam miliyan 17.

Hakan ne ya sa Tchouameni ya zama na hudu mafi tsada da kungiyar Santiago Bernabeu ta dauka a tarihi.

Cikin 'yan kwallon da Real Madrid ta saya mafi tsada da ke gaban dan kwallon Faransa, sun hada da Gareth Bale daga Tottenham a 2013 da Eden Hazard daga Chelsea a 2019 da kuma Cristiano Ronaldo daga Manchester United a 2009.

Daga nan sai Tchouameni a mataki na hudu da Real Madrid ta dauka da dan karen kudi, wanda ya ke na biyar kuwa shi ne dan wasan tawagar Colombia, James Rodriguez a 2014, bayan kammala gasar kofin duniya kan Yuro miliyan 75.

Haka kuma an tabbatar da cewar Tchouameni shi ne mafi tsada a Real Madrid a gurbin masu buga tsakiya, yana gaba da Zinedine Zidane, wanda ta dauka kan Yuro miliyan 73.5 a 2001 da kuma Kaka na Brazil da ta dauka a 2009 kan Yuro miliyan 65.

Har yanzu Eder Militao shi ne mai tsaron baya da aka dauka cikin masu tsada a Real Madrid, bayan da ta dauko shi daga Porto kan Yuro miliyan 50.