Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 09/06/2026.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Babangida, Muslim Muhammad Yusuf da Usman MINJIBIR

  1. 'An buɗe wuta kan masu zanga-zangar adawa da tsare mata a Afghanistan'

    Rahotannain sun ce dakarun Taliban a Yammacin Afghanistan sun buɗewa masu zanga-zangar rashin amincewa da tsare matan da suka ki sanya hijabi wuta.

    Rahotannin su kuma bayyana yadda mutum biyu suka mutu, yayin da aka kwantar da akalla uku da suka a asibiti.

    Yan sanda a birnin Herat sun ce masu zanga zangar sun karya doka saboda bijirewa sanya hijabi abin da ya ke wajibi ne a ƙasar.

    Al'ummar yankin sun ce a baya-bayan nan an tsare gomman matan da suka ƙi rufe jikinsu ko kuma suka bar gida ba tare da wani muharrami ba.

    An ce zanga-zangar ba ta yi tsayi ba, gaba ɗaya cikin minti 25 aka tarwatsa masu jerin gwanon da suka fara ta.

    Gwamnatin Taliban ta kuma musanta rahotannin kama matan.

  2. Trump ya ce Iran ce ta harbo helikwaftan Amurka kuma sai sun rama

    Shugaba Donald Trump ya zargi Iran da kakkaɓo wani jirgin helikwaftan Amurka a kusa da Mashigar Hormuz kuma ya lashi takobin ramuwar gayya ta hanyar hare-haren da suka "zama tilas".

    Wani jirgin ruwa maras matuƙi ne ya ceto ma'aikatan helikwaftan ƙirar Apache da ya faɗo ƙasa bayan harin, kamar yadda jami'an Amurka suka tabbatar wa BBC.

    "Matuƙan helikwaftan biyu abin ya ritsa da su, dukkansu kuma suna cikin aminci ba su ji rauni ba," shugaban na Amurka ya rubuta a shafinsa na Truth. "Duk da haka, Amurka jazaman, ya zame mata jazaman, ta mai da martani kan wannan hari."

    Wannan ne karon farko da Amurka ta yi asarar jirgin helikwafta ƙirar Apache tun bayan fara yaƙin da Iran kuma hakan ya zo ne bayan Trump tun da farko ya ce Washington tana cikin "matakan ƙarshe" na cimma yarjejeniya da Tehran domin kawo ƙarshen yaƙi.

  3. Har yanzu 'yan Najeriya da yawa na cikin matsi - IMF

    Asusun Lamuni na Duniya ya ce garambawul ɗin da gwamnatin Najeriya ta aiwatar ya ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasar, amma ya yi gargaɗin cewa fiye da kashi 60 na 'yan Najeriya a yanzu suna rayuwa cikiin fatara.

    Tun bayan hawansa kan mulki shekara uku da ta wuce, Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur mai tsada wanda ya sa tsawon shekaru gommai 'yan ƙasar ke shan man fetur da arha, sannan ya sassauta tsarin canjin kuɗi ga naira kuma ya yi wa harkar karɓar harajin Najeriya gyaran fuska.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito IMF na cewa yayin da masana tattalin arziƙi ke cewa ya dace a kawo manufar sauye-sauyen tun da daɗewa, amma talauci ya ci gaba da ƙaruwa, inda a ƙarshen shekara ta 2025 yake addabar kashi 63 na al'ummar Najeriya.

    Kuma sama da mutum miliyan 27 ne ke fama da rashin wadatar abinci a shekarar, in ji IMF.

    A cikin wata sanarwa bayan bitar tattalin arziƙin najeriya na shekara-shekara, IMF ya ce: "Har yanzu halin rayuwa ya kasance mai wahala ga 'yan Najeriya masu yawa".

    Ya ce talauci na ƙaruwa a ƙasar mafi yawan jama'a a Afirka tsawon shekaru, inda rahoton Babban Bankin Duniya na baya-bayan nan ya ce 'yan Najeriya kimanin kashi 61 ne ke rayuwa cikin talauci, sama daga kashi 40 na adadinsu a 2019.

  4. Kotu ta yanke wa tsohon minista hukuncin shekara 16 a Sri Lanka

    Wata kotu a Sri Lanka ta yanke wa wani tsohon ƙaramin minista hukuncin daurin shekara 16 bayan samun sa da laifin cin hanci da rashawa.

    Sarana Gunawardena, wanda ya yi minista a zamanin tsohon shugaban kasar Mahinda Rajapaksa, ya zamo daya daga cikin jami'an tsohuwar gwamnati da aka tsare.

    An yanke masa hukuncin daurin shekara hudu a kan laifuka hudu da aka same shi da su.

    An same shi da laifin karɓar cin hanci a hannun 'masu sayar da ababen hawa bayan ya yi aringizo wajen biyan su kudade kusan shekara 20 da ta wuce'.

  5. An yi wa Trump ihu a wajen wasan ƙwallon kwando a Amurka

    An yi wa shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ihu yayin da yake halartar wasan ƙwallon kwando a birnin New York, inda ya zama shugaban ƙasa na farko mai ci da ya taɓa halartar wasan ƙarshe na NBA Finals.

    Rahotanni sun ce an ji ihun ne daga magoya baya a filin wasan tsakanin New York Knicks da San Antonio Spurs, lokacin da kyamera ya haska hotonsa a babban allon filin wasa yana gaishe da jama’a yayin da ake rera waƙar ƙasar Amurka.

    Wasan, wanda shi ne na uku a jerin wasannin ƙarshe na bakwai, an buga shi a filin Madison Square Garden.

    Rahotanni sun bayyana cewa magoya baya da ke da tikiti sun shafe sa’o’i a layuka masu tsawo kafin shiga sakamakon tsauraran matakan tsaro da aka ɗauka saboda halartar shugaban.

    Trump ya halarci wasan tare da jikansa Kai Trump da wasu jami’an gwamnatinsa.

    Trump, wanda ya fito daga yankin Queens na New York, yana da doguwar tarihin rikici da birninsa na haihuwa, duk da cewa galibi birnin na nuna goyon baya ga jam’iyyar Democrat fiye da Republican.

  6. Najeriya za ta maida martani kan harin da ake kai wa ƴan ƙasarta a Afrika ta Kudu

    Najeriya ta ce tana nazarin matakan da za ta ɗauka kan Afrika ta Kudu, bayan samun rahotannin kai hare-hare kan ƴan ƙasarta da take shirin fara kwashe su a gobe Laraba.

    Ministar harkokin wajen Najeriyar Bianca Ojukwu ta ce gwamnatin ƙasar na duba yiwuwar mayar da martani kan abin da ke faruwa.

    Ministar ta ce duk da yake wannan matakin abu ne da za a cimma matsaya kansa nan gaba, amma ana ci gaba da tattaunawa kan abin da ya dace a yi.

    Ta zargi hukumomin Afrika ta Kudu da gaza yin komai kan hare-haren da ƴan ƙasarta ke kaiwa Ƴan Najeriya, inda ministar ta ce yawancin waɗanda ke zaune a can suna da takardu kuma sun cika duk wasu ƙa'idojin da suka kamata.

    Bianca ta ce sun samu bayanan yadda aka wawushe shagunan ƴan Najeriya da ke sana'o'insu a ƙasar, wasu kuma an cinna wa shagunan nasu wuta tare da haramtawa yaransu zuwa makaranta saboda yadda ake cin zarafinsu.

    Ta caccaki gwamnatin Afrika ta Kudu kan yadda har yanzu ba ta fito fili ta yi bayani da kakkausar murya ko ta ɗauki tsattsauran mataki kan abi da ke faruwa ba.

    Ministar ta ƙara da cewa Najeriya ba ta ji daɗin hakan ba, ganin yadda ta ba Afrika ta Kudu gudummuwa sosai wajen gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata a ƙasar.

    Kalama nata na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan ci rani ke ci gaba da zaman ɗarɗar a Afrika ta Kudu, inda ƴan ƙasar ke yin zanga-zangar ƙyamar baƙi da kuma buƙatar ƴan kama wuri zauna su bar ƙasar nan da 30 ga watan Yuni.

    Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da wasu matakai da ƙasar ke ɗauka wajen daƙile kwararar baƙin haure.

    Sai dai kuma ya gargaɗi ƴan ƙasarsa da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

  7. Somaliya ta nuna damuwa kan hana alƙalin wasa ɗan ƙasarta shiga Amurka

    Gwamnatin Somaliya ta bayyana “tsananin damuwa” kan yanayin da ya hana fitaccen alƙalin wasan ƙwallon ƙafa na ƙasa da ƙasa kuma ɗan ƙasarta, Omar Artan, shiga gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Amurka da Kanada da Mexico.

    Artan dai zai zama ɗan Somaliya na farko da zai yi alƙalancin wasa a babbar gasar ƙwallon ƙafa ta duniya.

    A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Somaliya ta fitar a ranar Talata, ta ce duk ƙoƙarin gwamnati, ciki har da tattaunawar diflomasiyya, bai yi nasarar tabbatar da tafiyar Artan Amurka ba.

    “Duk da haɗin gwiwar ma’aikatar harkokin waje da Tarayyar Somaliya da kuma ƙoƙarin ma’aikatar wajen tabbatar da cewa Artan ya halarci taron FIFA da sauran harkokin wasanni da za a gudanar a Amurka, hakan ya ci tura, har yanzu ba a warware matsalar ba, saboda haka alƙalin wasan bai samu damar tafiya ba,” in ji sanarwar.

    Gwamnatin ta bayyana Artan a matsayin abin alfahari ga ƙasar Somaliya, tana mai cewa halartar sa a matysayin alƙalin wasa a matakin duniya zai kasance dama ta nuna basirar ‘yan Somaliya tare da ƙara inganta martabar ƙasar a fagen wasanni na duniya.

    Gwamnatin ta sake jaddada goyon bayanta gare shi, tare da cewa za ta ci gaba da tallafa masa a harkokin ƙwarewarsa da kuma damar halartar gasanni na gaba a duniya.

  8. Shugaban China ya ziyarci Koriya ta Arewa bayan shekaru bakwai

    Shugaban ƙasar China, Xi Jinping, ya gana da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un a birnin Pyongyang, a ziyararsa ta farko cikin shekaru bakwai.

    Kafofin yaɗa labaran Koriya ta Arewa sun bayyana cewa ganawar ta buɗe sabon babi a dangantakar ƙasashen biyu, inda aka cimma matsaya kan ƙara haɗin gwiwa a fannoni na siyasa, tattalin arziki da al’adu.

    An kuma jaddada ƙarfafa musayar ziyara tsakanin manyan jami’an gwamnati.

    Kim Jong Un ya bayyana goyon bayansa ga manufar “One China”, wadda China ke amfani da ita wajen ɗaukar Taiwan a matsayin ɓangaren ƙasarta.

    Rahotanni dai ba su ambaci batun shirin makamin nukiliya na Koriya ta Arewa ko dangantaka da Amurka ba, abin da ke nuna China na son mayar da hankali kan dangantakar cikin gida tsakanin ƙasashen biyu.

  9. Tinubu ya rantsar da sabbin ministoci biyu

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da sabbin ministoci biyu, inda ya naɗa Joseph Tegbe a matsayin ministan Lantarki da Sola Enikanolaiye a matsayin ƙaramin ministan harkokin waje.

    An gudanar da bikin rantsarwar ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a gaban iyalan ministocin da manyan jami’an gwamnati.

    Joseph Tegbe, wanda ya fito daga Ibadan a Jihar Oyo, ƙwararren masani ne a fannin sauye-sauyen tattalin arziki da harkokin kuɗi da tsarin hukumomi, tare da gogewar aiki sama da shekaru 35 a gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

    Sola Enikanolaiye kuma ɗan asalin Igbagun a Jihar Kogi ne, kuma ƙwararren jami’in diflomasiyya da ya yi fice a harkokin waje. Ya kammala digiri na farko a jami'ar Ahmadu Bello da sakamako mafi kyau, sannan ya samu digiri na biyu a fannin Dokar Ƙasa da Harkokin Diflomasiyya daga jami'ar Legas.

    Dukkanin su an bayyana su a matsayin ƙwararru da suka samu horo da ƙwarewa mai zurfi a fannoni daban-daban na gudanar da gwamnati da hulɗar ƙasa da ƙasa.

  10. Muna da muradu iri ɗaya da Isra’ila amma su kan bambanta - Amurka

    Mataimakin shugaban ƙasar Amurka, JD Vance, ya ce ƙasar Amurka da Isra’ila suna da muradun da dama iri ɗaya amma akwai lokuta da manufofinsu ke bambanta.

    Da yake magana da tashar Fox News a ranar Litinin, Vance ya bayyana cewa manufofin Washington kan Iran za su ci gaba da bin abin da shugaban ƙasa Donald Trump ke ganin ya fi dacewa ga Amurka.

    “Muna da muradu iri ɗaya da Isra’ila,” in ji shi, “amma akwai lokuta da muradunmu ke bambanta.”

    Ya ƙara da cewa babban burin Amurka shi ne tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba.

    A cewarsa, gwamnatin Amurka ta samar da yanayi da zai iya kai wa ga cimma matsaya mai ɗorewa kan batun nukiliyar Iran.

    Sai dai ya ce irin wannan matsaya na iya zama abin da Isra’ila za ta amince da shi ko kuma ba za ta gamsu da shi ba, amma Amurka za ta ci gaba da bin abin da ta ɗauka mafi amfani ga ƙasarta.

    “Isra’ila za ta iya so hakan ko kuma ba lallai ta so ba, amma mu a matakin ƙarshe muna ganin wannan shi ne mafi alheri ga Amurka,” in ji shi.

    Ya ce Amurka za ta ci gaba da ƙoƙarin cimma wannan buri, yana mai jaddada cewa shugaban ƙasa ne aka zaɓa domin aiwatar da manufofin da suka dace da muradun ƙasar."

  11. An ci gaba da yaƙi a Lebanon duk da yarjejeniyar tsagaita wuta

    Isra'ila da Hezbollah a Lebanon sun ci gaba da musayar wuta a tsakaninsu duk da cewa akwai yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Kafofin yaɗa labaran Lebanon sun ruwaito cewa aƙalla mutum uku aka kashe a hare-haren Isra'ila a kudancin ƙasar da safiyar yau Talata.

    Wannan na zuwa ne bayan da Iran da Isra'ila suka kai wa junansu hare-hare a karon farko duk da yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Afrilu.

    Daga nan ne Isra'ila ta kai hari kan Lebanon, inda ƴan Hezbollah suka mayar da martani.

    Amurka ce ta shiga tsakani wajen tsagaita wutar a ranar 16 ga watan Afrilu, inda duka ɓangarorin ke zargin juna da karya ka'idojin yarjejeniyar.

  12. Ƴanbindiga sun buƙaci miliyan 100 kafin sako dattijan da suka je sulhu a Zamfara

    Ƴan bindigar da suka yi garkuwa da mutum kusan 40 bayan sun tafi yin sulhu da yanfashin daji a ƙaramar hukumar Maradun na Jihar Zamfara sun buƙaci a biya naira miliyan 100 kafin su sako su.

    Mutanen da aka yi garukuwar da su a ranar Lahadi da yamma galibinsu dattawa ne, kamar yadda danmajalisar dokokin jiha mai wakiltar yankin na Maradun Maharazu Salisu ya shaida wa BBC.

    Lamarin ya faru ne a ƙauyen Magamin Diddi wanda rahotanni suka ce yana a kusa da ɗaya daga cikin dazukan da ƴan fashin daji ke da sansani

    A tattaunawarsa da BBC, Sunusi Ahmed Dosara ya ce: "Tun wata uku da suka wuce (ɓarayi) sun hana su (ƙauyen) zaman lafiya, ana cikin haka ne sai ɓarayin suka kwaɗaita musu cewa su zo a yi sulhu domin su bar su, su riƙa cin kasuwa.

    "To daga nan sai dattijai suka je daji domin haɗuwa da ƴan bindiga, amma a lokacin da suka je sai ɓarayin suka riƙe su, sanan suka sako wasu daga cikinsu suka ce ba za su sake su ba sai an cika musu wasu sharuɗaɗa".

    Shugaban ƙaramar hukumar ya ce daga ƙididdigar da suka yi mutanen da ƴan fashin dajin suka riƙe "sun kai 39".

    Ya ƙara da cewa dukkanin mutanen da ake riƙe da su "maza ne dattawa".

  13. Mutum 3 sun mutu a hatsarin jirgin ƙasa a Najeriya

    An tabbatar da mutuwar mutum uku a wani hatsarin jirgin ƙasa a Najeriya, inda kusan mutum 40 suka jikkata.

    Kamar yadda hukumar kula da sufurin jiragen ƙasan Najeriya, NRC ta tabbatar, lamarin ya faru ne a jiya Litnin kuma fasinjoji da dama sun samu raunuka.

    Rahotanni sun ce jirgin ƙasa ya sauka daga kan layinsa ne a hanyar Warri zuwa Itakpe cikin yankin Agbor na jihar Delta a kudancin ƙasar.

    A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce tuni ta tura jami'an kai ɗaukin gaggawa da sauran hukumomin da abin ya shafa zuwa wurin da taragan jirgin suka sauka domin ba da taimakon da ya wajaba.

    Sai dai ana fargabar adadin waɗanda suka mutu ya haura uku, kamar yadda wasu ganau suka bayyana.

    Shugaban ƙaramar hukumar Ika North-East Mr. Monday Odigwe, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa sama da fasinjoji 35 sun jikkata, inda ake ci gaba da duba su a asibiti.

    Gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori ya yi jaje ga waɗanda lamarin ya rutsa da su.

    Sufurin jirgin ƙasa a Najeriya ya yi matuƙar taɓarɓarewa, inda ake yawan samun faɗuwar taragai daga kan layin dogo,a wasu hanyoyin ma jiragen kwata-kwata ba sa aiki.

    A ranar 26 ga watan Agustan 2026 ma, wani jirgin ƙasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ya faɗi jim kaɗan bayan barinsa Abuja.

  14. Jirgin Amurka ya faɗo a kusa da Mashigar Hormuz

    Rahotanni sun ce wani jirgin helikwafta na sojin ƙasar Amurka ya faɗo a kusa da Mashigar Hormuz.

    Jaridar New York Times ta ruwaito cewa "wasu majiyoyi" biyu sun shaida mata cewa jirgin ya faɗo ne a jiya Litinin, kuma a ceto duka mutane biyu da ke cikin jirgin.

    Sai dai ba a tabbatar ko dakarun Iran ne suka harbo jirgin ba, ko kuma ya samu tangarɗar na'ura ne.

    Shugabanm Amurka Donald Trump ya sanar da cewa duka matuƙan jirgin "suna cikin ƙoshin lafiya"

    "Babu wanda ya ji rauni," in ji Trump.

    Ya ƙara da cewa gwamnati za ta saki cikakken rahoto game da lamarin a yau Talata.

  15. Netanyahu bai yi biris da umarni na ba - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada cewa firaministan Isra’ila bai yi biris da umarninsa ba, na dakatar da kai hari kan Iran a ranar Litinin.

    Da yake magana da BBC, Trump ya ce sai da aka harba makamai masu linzamin sannan ya shaidawa Benjamin Netanyahu kada ya mayar da martani ga hare-haren Tehran.

    A yanzu dai Iran da Isra’ila sun dakatar da kai wa juna hare-hare, to amma sun yi gargadin cewa za su iya komawa faɗan idan lamarin ya sake taɓarɓarewa.

    Tehran dai ta yi barazanar daukar ƙwararan matakai a kan Isra'ila idan har aka ci da kai hare hare a Lebanon, inda sojojin Isra'ila ke faɗa da ƴan Hezbollah.

    A ranar Lahadi ne Isra'ila ta kai hari kan wurin da Hezbollah ke da karfi a kudancin Beirut, inda su ma ƴan Hezbollah suka mayar da martani ta hanyar harba makaman roka.

  16. Assalamu Alaikum!

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye.

    Kamar kullum, yau ma za mu muku labaran abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da wasu muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a wannan rana ta Talata.

    Za ku iya yin tsokaci a shafukanmu na sada zumunta: Facebook, X, instagram, YouTube da kuma zaurenmu na WhatssApp.