Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Istanbul Basaksehir ta dauki Mesut Ozil
Mesut Ozil ya koma Istanbul Basaksehir, bayan da Fenerbahce ta soke kwantiragin da ke tsakaninta da tsohon dan kwallon tawagar Jamus.
Basaksehir ta sanar da cewar dan wasan mai shekara 33, ya amince da kunshin yarjejeniyar wata 12 a kungiyar ta Turkiya.
Ozil ya koma Fenerbahce a matakin wanda bai da kwantiragi daga Arsenal a Janairun 2021, wanda yarjejeniyarsa ya kamata ta karkare a kungiyar Turkiya a karshen kakar 2024.
Sai dai kuma rabon da Ozil ya buga tamaula a Fenerbahce tun cikin watan Mayu, bayan da kungiyar ta daina saka shi a wasanni.
Ozil ya buga wasa 37 a kaka daya da rabi a Fenerbahce da cin kwallo tara, tun bayan da y7a koma kungiyar a 2021, bayan da yarjejeniyarsa ya kare a Arsenal.
A watan Yuni Fenerbahce ta maye gurbin kocin rikon kwarya, Ismail Kartal da dan kasar Portugal, Jorge Jesus.