Watakila Arsenal ta yi kaka ta 21 ba ta dauki Premier League ba

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta barar da damar hawa kan teburin Premier League ranar Lahadi, bayan da ta yi rashin nasara 2-0 a hannun Aston Villa a Emirates.

Aston Villa karkashin tsohon kociyan Gunners, Unai Emery ta doke Arsenal gida da waje kenan a bana, bayan cin 1-0 ranar 9 ga watan Disambar 2023 a Villa Park.

An kuma ci Arsenal kwallayen biyu daf da za a tashi ta hannun Leon Bailey a minti na 84 da Ollie Watkins saura minti uku a busa tashi.

Da wannan sakamakon Gunners mai maki 71 iri daya da na Liverpool ta ukun teburi, Manchester City tana da maki 73 ta dayan teburi da tazarar maki biyu tsakaninsu.

Ranar Asabar Manchester City ta dura 5-1 a ragar Luton Town a Etihad a ranar Crystal Palace ta ci Liverpool 1-0 a Anfield a karawar mako na 33.

Wannan shi ne karon farko da aka ci Arsenal a 2024 cikin wasa 11 a Premier League, wadda ta tashi ba ci da Manchester City, sannan ta lashe sauran wasannin.

Rabonda Arsenal ta dauki Premier League tun kakar 2003/04 mai 13 jimilla, tun daga nan ba ta sake lashe kofin ba.

Kungiyar dake Emirates ta kare kakar bara ba tare da daukar kofi ba, bayan da Manchester City ta sha gaban Arsenal a Premier daga karshe-karshen gasar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hakan ya bai wa City damar lashe kofi uku ciki har da na FA Cup da kuma Champions League karon farko a tarihi.

Arsenal za ta je Jamus, domin buga wasa na biyu a Champions League da Bayern Munich ranar Laraba zagayen quarter finals.

Ranar Talata Arsenal ta tashi 2-2 da Bayern Munich a Emirates a wasan farko, duk wadda ta samu nasara a Jamus za ta kai daf da karshe a gasar zakarun Turai.

Arsenal ba ta taba lashe Champions League ba, yayin da Bayern Munich take da shida jimilla.

Saura wasa shida Gunners za ta buga nan gaba, ciki har da karawa da Chelsea da Tottenham da kuma Manchester United, inda ake tunanin za ta iya kara barar da maki.

Wasannin da suke gaban Arsenal a Premier League:

20 ga watan Afirilu - Wolves ( Molineux)

23 ga watan Afirilu - Chelsea (Emirates)

28 ga watan Afirilu - Tottenham (Tottenham Stadium)

4 ga watan Mayu - Bournemouth (Emirates)

12 ga watan Mayu- Manchester United (Old Trafford)

19 ga watan Mayu - Everton (Emirates)