Liverpool za ta je gidan Arsenal don buga Premier ranar Lahadi

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan mako na 23 a Premier League da za su kara ranar Lahadi a Emirates.
Liverpool ce ta daya a kan teburin Premier da maki 51, ita kuwa Arsenal mai maki 46 iri daya da na Manchester City tana matsayi na uku.
Sun fara haduwa a Premier League ta bana ranar 23 ga watan Disambar 2023, inda suka tashi 1-1 a Anfield.
A wasa na biyu kuwa Liverpool ce ta je Emirates ta fitar da Arsenal daga FA Cup da cin 2-0 ranar 7 ga watan Disambar 2024
Ɗan wasan Arsenal, Thomas Partey ya ci karo da koma baya a shirin da yake na warkewa daga raunin da yake jinya.
Har yanzu Takehiro Tomiyasu yana wakiltar kasarsa, Japan, sai dai Gabriel Jesus ya warke bayan raunin gwiwa.
Ɗan kwallon Liverpool, Darwin Nunez za a auna koshin lafiyarsa, bayan raunin da ya ji a karawa da Chelsea a Premier a tsakiyar mako.
Watakila Alexis Mac Allister ya buga wasan, amma Wataru Endo da Stefan Bajcetic da Mohamed Salah da Kostas Tsimikas ba za ba buga fafatawar ta hamayya ba.
Abinda ya kamata ku sani a karawa tsakanin kungiyoyin:
Wannan shi ne wasa na biyar a gasar lik din Ingila da tsakanin kungiyoyi biyu da za su hadu karo na 200.
Wasa biyu Arsenal ta ci daga 17 a lik da ta fuskanci Liverpool, inda ta yi nasara a Emirates a Yulin 2020 da kuma a Oktoban 2022.
Liverpool ta zura kwallo 53 a ragar Arsenal a dukkan fafatawa karkashin jagorancin Jurgen Klopp.
An zura kwallo 186 a raga a Premier League a wasan hamayya tsakanin Arsenal da Liverpool.
Kungiyar Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta ci dukkan wasa bakwai a Premier League da ta yi a gida a bana tsakaninta da kungiyoyi daga wajen Landan.
Cikin wasa 54 da aka doke Mikel Arteta a matakin kociyan Arsenal a dukkan karawa, Manchester City ta yi nasara tara da Liverpool mai shida.
Kwallo uku baya da Arsenal ta zura a ragar Liverpool an ci mata su ta hannun Gabriel Martinelli da Gabriel Jesus da kuma Gabriel.
Martinelli yana da hannu a kwallo shida da aka ci Liverpool, wanda ya zura hudu ya kuma bayar da biyu aka zura a raga.
Kungiyar Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta barar da maki a wasa uku a lik a bana da ta kara da wadanda ke cikin ƴan hudun farko a makon wasannin da za ta fuskanta.
Sun ci wasa shida a waje a lik a bana, a kakar da ta gabata irin yawan nasarar da ta yi kenan wato a 2022-23.
Ta ci kwallo hudu a dukkan karawa uku da ta yi a lik a 2024.
Liverpool na fatan kada ta yi rashin nasara a gidan Tottenham da Arsenal a kaka daya, rabonda ta yi hakan tun 2009-10.
Wasa biyar ta ci daga 16 baya da take ziyartar birnin Landan buga tamaula.
Sau tara Darwin Nunez na buga kwallo na dukan turke a kakar nan.










