Alaba ya fadi dalilin da ya zabi Messi maimakon Benzema

Asalin hoton, Getty Images
Kyaftin din Austria, David Alaba ya ce tawagar shi ce ta cimma yarjejeniyar zabar Lionel Messi, maimakon takwaransa Karim Benzema.
Ranar Litinin Messi dan kwallon Argentina mai taka leda a Paris St Germain ya lashe kyautar gwarzon kwallon kafa na duniya na Fifa na 2022.
An ta caccakar mai tsaron baya Alaba, mai shekara 30 a kafar sada zumunta, bayan da bai zabi Benzema ba.
Messi ya yi nasara kan takarar da ya yi tare da Benzema na Real Madrid da Kylian Mbappe na Paris St Germain a bikin da aka yi a birnin Paris din Faransa.
''Tawagar Austria ce ta yanke shawarar zaben ba radin kaina bane ni kadai'' in ji Alaba.
Fifa ce ta fitar da sakamakon wadanda suka kada kuri'a, inda aka ga Alaba ya zabi Messi a matakin na farko, sai Benzema na biyu, sannan Mbappe na uku.
Benzema da Alaba na taka leda tare a Real Madrid tun bayan da kyaftin din Austria ya koma kungiyar daga Bayern Munich a 2021.
''Kowa ya san yadda nake, musamman Karim ya san ina kaunarsa da rawar da yake takawa, kuma na sha fada cewar daya ne daga fitattun masu cin kwallaye a duniya, ba wata tantama,'' in ji Alaba.
Ana yin zaben ne tsakanin kociyan tawagar kasa mamba ga Fifa da kyaftin da 'yan jarida da magoya baya tamaula a fadin duniya.










