Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afcon 2023: Salah ya koma Liverpool domin a duba raunin da ya ji
Mohamed Salah ya koma Liverpool daga sansanin Masar a Afcon, domin a duba raunin da ya ji a gasar cin kofin Afirka da ke gudana a Ivory Coast.
Kyaftin ɗin Masar na fatan komawa cikin tawagar, domin buga mata karawar daf da karshe idan ƙasar ta kai zagayen.
Salah ya ji rauni a karawar hamayya da Masar ta tashi 2-2 da Ghana ranar Alhamis a wasan zagaye na biyu na cikin rukuni.
Masar za ta fafata da Cape Verde ranar Litinin a wasan karshe na cikin rukuni, kuma idan ta yi nasara a karawar za ta kai zagaye na biyu a gasar.
Tun farko hukumar kwallon kafa ta Masar ta sanar cewar Salah ba zai buga wasa biyu ba, tana sa ran cewa zai koma taka leda a zagayen quarter final ranar 2 ko kuma 3 ga watan Fabarairu, idan ta kai ga matakin.
A ranar ta Juma'a kociyan Liverpool ya sanar da cewa Salah ya ji rauni ne sakamakon wasa da yawa da ya buga, wanda a shekara shida, karawa 10 ce ya yi hutu a lik.
Rabon da Masar ta lashe kofin Afirka tun 2010, shekara ɗaya kafin Salah ya fara buga wa tawagar wasanni.
Masar tare da Salah ta kai wasan karshe a 2021 a Kamaru, inda Senegal ta lashe kofin a bugun fenariti, haka kuma ta yi ta biyu a 2017.
Salah shi ne ya ci wa Masar kwallo ta biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga da suka tashi 2-2 da Mozambique a wasan farko a rukuni na biyu a Afcon.
Salah ya ce yana sa ran zai lashe kofin Afirka nan gaba kaɗan.