Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An samu ɓaraka tsakanin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Amurka da Isra'ila
Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Amurka, Chuck Schumer, ya yi kira da a yi sabon zabe a Isra'ila, yana mai bayyana Firaminista Benjamin Netanyahu a matsayin mai hana ruwa gudu ga zaman lafiya.
Mr Schumer, dan jam'iyyar Democrat kuma Bayahude mafi girman mukami a Amurka, wanda ya dora alhakin yakin Gaza a kan hamas, amma ya ce, ransa ya baci saboda Isra'ila ta hallaka Falasdinawa da yawa wadanda ba su ji ba ba su kuma gani ba.
Kalaman na Chuck Schumer, wata alama ce ta samun baraka a abotar da za a ce ta kut da kut, kafin yanzu.
Mista Schumer, ya nemi da a yi sabon zabe a Isra’ilar domin raba kasar da mulkin Firaminista Benjamin Netanyahu, wanda ya ce ya zama karfen kafa ga duk wani yunkuri na neman zaman lafiya, wanda kuma ya ce ya bata.
Ya ce ba karamin kuskure ba ne Isra’ila ta yi watsi da yarjejeniyar kafa kasa biyu da Falasdinawa a kan rikicin.
Shugabanni a Amurka dai na kokarin kauce wa suka na kai tsaye ga yadda Netanyahu ke tunkarar rikicin na Gaza.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Matthew Miller, y ace kalaman na Sanata Schumer, ra’ayinsa ne ba matsayin gwamnatin Biden ba:
Ya ce: ''Ba shakka majalisar dokoki reshe ne na gwamnati mai zaman kansa, ina ganin gwamnatin Isra’ila ta fahimci sosai yadda gwamnatin Amurka ke aiki, suna ganawa akai-akai, ba kawai da ‘yan bangaren zartarwa ba, har ma da ‘yan majalisun dokoki, ciki har da Sanata Schumer, wanda ya je Isra’ila a lokuta da dama a cikin shekaru, kuma na tabbata sun fahimci cewa wannan magana ce ta kashin kansa.''
To amma wadannan kalamai daga bakin daya daga cikin manyan kusoshi a Amurkar, na nuna karara sabani a yadda tafiyar kasashen biyu ke kasancewa kan yakin.
Da yake jawabi a zauren majalisar dattawan a jiya Alhamis, Mista Schumer, wanda tsawon shekara 25 da yake a majalisar yake goyon bayan Isra’ila, ya yi gargadin cewa yawan mutanen da Isra’ila ke jikkatawa da kashewa a Gaza, ka iya sa a mayar da ita saniyar-ware.
Ya yi kakkausan suka ga Mista Netanyahu da cewa ya bayar da fifikon tsiransa a siyasa fiye da muradin Isra’ila.
Ya ce dole ne Isra’ila ta yi gyara, ta dauki matakan kare farar hula a Gaza.
Sai dai nan da nan jagororin Isra’ilar ba tare da wani jinkiri ba suka mayar wa da Mista Chuck Schumer martani da cewa, Isra’ila ba wata karamar kasa ba ce, da ke zaman kamar rakumi da akala.
Kuma jam’iyyar Firaministan, Likud ta ce, manufofi da tsare-tsaren Netanyahun na da goyon bayan mafiya rinjaye a kasar.
Duk da cewa Amurka na ci gaba da zama babbar kawar Isra’ila kuma wadda ta fi ba ta taimakon soji, ana kara samun damuwa a gwamnatin ta Joe Biden har ma a tsakanin ‘yan jam’iyyar tasa a kan yadda Isra’ila ke tafiyar da yakin na Gaza
Mista Biden, wanda zai kara takarar shugabancin Amurkar na fuskantar matsin lamb ana siyasa a wannan takar a kan yakin.
Baraka ta fara fitowa fili tsakamin gwamnatocin biyu kawaye a ‘yan makonnin nan, inda Mista Biden ke gargadin Isra’ila a kan fadada yakin zuwa cikin birnin Rafah.
Sai a watan Oktoba na 2026 ne dai za a yi zaben gama-gari a Isra’ila.