Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ne ke shan wuyar yaƙin Gaza

An wallafa

Kamal Karaja ma'aikacin wani kamfanin gini ne a Isra'ila, yana kuma samun dalar Amurka 3,500 ko wanne wata - wannan albashi ne mai kyau ga Bafalasdinen da yake zaune a Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Amma tun bayan fara rikicin Hamas da Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, da kuma hare-haren ramuwar da Isra'ila ke kaiwa, aka kwace izinin da yake da shi na aiki a Isra'ilan, jami'an tsarin Isra'ila na cewa an yi haka ne saboda tsaro.

"Ina ta jiran yaƙin ya ƙare amma har yanzu shiru," in ji matashin mai shekara 32, da ke zaune a garin Deir Bzi a wajen yankin Ramallah.

"Sai da na sayar da motata bayan kwashe wata guda ana wannan rikici, saboda matsalar kuɗi."

Hukumomin Falasɗinawa sun ce lamarin ya shafi ma'aikata 200,000 wadanda mafi yawansu ke zaune a Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Kamal ya ce sai da 'yarsa 'yar shekara uku Zein "ta gano bana iya sayan kayan abinci da na marmari kamar yadda na saba a baya".

"Sai da ta tambaye ni me yasa ba na sayo mata alewa da kayan dadi kamar da."

Dubban mazaje da garin da Kamal ke zaune suna gida saboda irin wannan dalili - dan haka dole tattalin arziki ya shiga matsala.

Bayan shafe watanni yana neman aiki, Kamal ya sama aikin mako biyu a wani kamfanin gini da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan.

Amma haka wanda ya ɗauke shi aiki ya rabu da shi saboda ba zai iya ci gaba da biyan shi ba.

Yanzu ya fara sare bishiya yana sayar da itacen ga mutanen da ke da buƙata.

"Abin da nake samu a itacen da nake yi bai fi kashi biyu ba cikin dari na abin da nake samu a Isra'ila," in ji Kamal.

Ba a ba shi wani abu na diyya ba daga hukumomin kamfanin da yake aiki lokacin da suka kwace takardar izininsa ta aiki a Isra'ila.

Kamar yadda ake ɗaukar sauran Falasɗinawa aiki, shi ma haka aka ɗauke shi ba tare da yarjejeniya ba.

Makomar ma'aikatan kasashen waje

Akwai mutum ɗaya cikin Falasɗinawa biyar da ke aiki a Isra'ila ko kuma wuraren da Isra'ila ta yi gine-ginenta a Gabar Yammacin Kogin Jordan kafin wannan rikici - kamar yadda ƙididdigar hukumomin Falasdinawa suka bayyana.

Wannan gine-gine da Isra'ila ta yi Gabar Yammacin Kogin Jordan haramtacce abu ne a dokar duniya, ko da yake ita ta musanta hakan.

Ma'aikatan na taimakawa wajen ci gaban tattalin arzikin Falasdinawa da dala biliyan 3.2 duk shekara, kuma mafi yawansu a kamfanin gine-gine suke aiki.

Wasu kamfanonin da ke kasuwanci da Isra'ila na ta kamun kafa don a bar Falasdinawan su koma bakin aikinsu, amma gwamnati ta zo da wani shiri na daban.

Tana so ta maye gurbin alasdinawan da ke mata aiki da ma'aikata sama da 60,000 daga ƙasashen India da China da Moldova da Sri Lanka da kuma Thailand a wannan shekarar.

Shugaban cibiyar kasuwancin Falasdinawa Shaher Saad ya yi tir da wannan matakin na Isra'ila.

"Akwai kimanin Falasdinawa 105,000 da ake aiki a kamfanin gine-gine na Isra'ila," kamar yadda Shaher ya shaida wa BBC Arabic, inda ya ce yanzu duk suna zaune ba su da aikin yi.

Ɗauke wuta da yanke ruwa

Bassam Karaja wani Bafalasdine ne da ba shi da alaka da Kamal, yana zaune a Ramallah da 'ya'ya hudu, ya tsinci kansa cikin talauci tun bayan karbe izininsa na aiki.

Baya iya biyan kuɗaɗen wuta da na ruwa, hakan ya sa aka yanbke masa wuta da ruwa.

"Bana makara wajen biyan kudaden wuta da na ruwa tsawon shekara 10 da na yi ina aiki a Isra'ila," in ji Bassam.

"Amma inda daina aiki na daina samun wuta da ruwa."

Bassam yana samun dala 4,000 a wata lokacin da yake aiki.

Ya ce watanni hudun da suka gabata sun fi kowanne tashin hankali tun bayan na Korona, lokacin da yake aiki na ɗan lokaci.

Bassam ya zargi hukumomin Falasdinu da watsi da ma'aikata da suke taimakawa wajen samar musu da kudin shiga.

Tun bayan fara rikicin yawan adadin marasa aikin yi ya kai kashi 47 daga 23 a yankin Falasdinu.

Tun gabanin rikicin dama hukumomin Falasdinawa suna cikin matsalar kudi, to da rikicin sai abun ya sake tsananta.