Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ba za ta ɗaga ƙafa ba - Arteta
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya gamsu da nasarar da ƙungiyarsa ta samu a kan Sheffield United da ci 6-0, kuma ya ce ƙungiyar na buƙatar ta ci gaba da taka rawar gani a sauran wasannin kakar wasan bana.
Arsenal ta yi nasara karo na bakwai a jere a gasar Premier League, bayan da ta yi wa Sheffield United dakan sakwara a filin wasan Bramall Lane, kuma Arteta ya ce ƴan wasansa na da niyyar ci gaba da samun irin waɗannan nasarorin a gasar Premier League ta bana.
Ya shaida wa BBC cewa: "Mun yi ƙoƙari sosai kuma babban sakamako ne a gare mu, ga kuma yawan ƙwallayen da muka zura tare da hanawa a ci mu. Tawagar na nuna alamun ci gaba a haka.''
Gunners sun zura ƙwallaye uku cikin mintuna 13 kuma an tafi hutun rabin lokaci suna cin ƙungiyar da ke kurar baya a gasar da ci 5-0.
Martin Odegaard da Gabriel Martinelli da Kai Havertz da Declan Rice da Ben White ne suka zura kwallayen.
Nasarar ta tabbatar da cewa Arsenal ta ci gaba da kasancewa ta uku a kan teburi da maki biyu tsakaninta da Liverpool da ke matsayi na ɗaya, inda ya rage sauran wasanni 11a kakar wasan bana.