Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me zai faru a jihar Ribas bayan soke ‘yan takara ta APC
Babbar Kotun Tarayya a birnin Fatakwal ta soke zaben fitar a gwamni da jam’iyyar APC ta gudanar a Ribas kan saɓa dokoki wajen ware wasu mambobinta a matsayin deleget a lokacin zaɓen.
Wani mai suna George Orlu da wasu mutum hudu da suka ce sun saye fom din zaɓen fitar da gwani, su ne suka shigar da kara kotu da bukatar a soke zaɓen bayan sun zargi cewa an waresu a lokacin kada kuri’a.
Mai shari’a E.A. Obile a lokacin yanke hukunci ya ce babu shaka an aikata ba daidai ba wajen ware mutane daga kada kuri’a a zaɓukan fitar da gwanin.
Mai shari’a Obile ya soke zaɓukan baki daya, don haka a yanzu ba a yi musu kallon ‘yan takara a zaɓen 2023 da ke tafe.
Za mu daukaka kara, in ji APC reshan Ribas
Amma dai jam’iyyar APC a Ribas ta faɗawa mamobinta su kwantar da hankalinsu, yayinda ta take kalubalantar hukuncin kotun.
A wata sanarwa da kakinta na jihar Ribas ya fitar, kan daukaka karar, Tonye Cole na kwamitin yaƙin neman zaɓen Sogbeye Eli, na cewa mai shari’a ya amince da masu shigar da kara duk da cewa akwai shaidu da suka gabatar da ke nuna cewa ba ‘ya’yan jam’iyyar ba ne.
Ya kuma shaida cewa tuni shirye-shirye su ka kammalu, kuma suna da yaƙinin cewa za su yi nasara a kotun daukaka kara, da kuma dawo da sunayen ‘yan takararsu kafin ranar zaɓe.
Shin tarihi na neman sake maimaita kansa ne?
Wannan lamari da ake ciki a yanzu na sake tunasar da makamacin wannan yanayi da ya faru a Ribas a zaɓen 2019, lokacin da kotu ta umarci hukumar zaɓe ta INEC ta cire sunayen ‘yan takarar APC daga babban zaɓe.
A wannan shekarar, bangare biyu da jam’iyyar APC ta kasaftu kowanne ya gudanar da zaɓensa na fitar da gwani daban, inda ya kasance an samu ‘yan takara biyu daga jam'iyya guda kuma ke naman kujera ɗaya.
Bangaren da ke biyayya ga tsohon ministan sufuri, Chibuike Amaechi ya yi nasa zaɓen fitar da gwanin, da ya bai wa Tonye Cole nasara a takarar gwamna.
Daya ɓangaren kuma da ke biyayya ga Sanata Magnus Abe su ma sun yi nasu zaben tare da tsayar da Sanata Abe a matsayin dan takararsu na gwamna.
Wannan batu ya kai gaban kotun daukaka kara da kuma Kotun Koli, abin da ya kai ga an soke zaɓukan baki ɗaya kan dalilan saɓa dokokin zaɓe da raina umarnin kotu.
Amma a watan Fabarairu 2019, Kotun Koli ce ta hana APC takara a zaɓe 2019 a Ribas.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan kotun daukaka kara ta umarci Inec ta haramtawa ‘yan takarar APC neman kowacce kujera a lokacin zaɓuka.
Kotun daukaka kara a ranar 4 ga watan Fabarairu ta dakatar da hukuncin da babbar kotu ta yanke na soke dukkanin zaɓukan fitar da gwani APC a Ribas.
Kotun koli kuma ta nuna goyon-bayanta ga hukuncin babbar kotun tarayya a Fatakwal da ya dakatar da APC daga shiga babban zaɓe a Ribas.
Da wannan hukunci, APC ba za ta iya shiga takara a babban zaɓen ranar 16 ga watan Fabarairu ba, na ‘yan majalisar wakalai 13 da Sanatoci 3 a jihar Ribas.
Babbar kotun jihar kuma ta soke dukkanin tikitin takarar mambobin APC a Ribas a ranar 7 ga watan Janairun 2019.
A ranar 7 ga watan Janairun 2019, Babbar kotun Tarayya a Fatakwal, ta umarci INEC da kada ta kuskura ta amince da kowanne ɗan takara na APC a babban zaɓen 2019 a faɗin Ribas.
Kotun ta kuma soke dukkanin wani goyon-baya da APC ta samu a jihar Ribas kan batun zaɓukan 2019.
Kotun ta shaida karara cewa APC ba za ta shiga takarar kujerar gwamna ba da kujerar Sanatoci, da kuma majalisar wakalai da kuma na ‘yan majalisar jiha a zabukan 2019.
Ko daukaka karar da suka yi kan batun takarar gwamna ta Tonye Cole da sauransu, bayan kwamitin da shugaban kasa ya kafa na shari’a bai iya warware wannan matsala ba.
Wannan dambarwa ita ta haifarwa APC tarnaƙi da hanata, damar shiga a fafata da ita a zaɓukan 2019.
To shin tarihi na neman sake maimaita kansa ne? BBC za ta cigaba da sa ido domin ganin yada za ta kaya.