Eden Hazard ya yi ritaya

An wallafa

Tsohon dan kwallon Chelsea, Eden Hazard ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa, bayan ya bar Real Madrid a karshen kakar wasan da ta wuce.

Hazard mai shekara 32, ya koma Real ne daga Chelsea a shekara ta 2019 a kan fam miliyan 89, amma wasa 54 na lig kawai ya bugawa kungiyar.

Ya lashe kofin gasar firimiya biyu a Stamford Bridge.

"Dole ne ka saurari kanka, kuma ka daina buga kwallo a lokacin da ya dace," in ji Hazard wanda tun a watan Yuni ba shi da kulob.

"Bayan shafe shekara 16 tare da buga wasa 700, na yanke shawarar daina buga kwallon kwararru."

Dan kwallon Belgium din ya yi ritaya daga buga wa kasarsa kwallo a watan Disamban bara, bayan an fitar da kasar a zagayen farko na gasar cin kofin duniya.

A Real Madrid, Hazard ya lashe kofin zakarun Turai da kofin Super Cup da La Liga sau biyu da Copa del Rey sau daya.

Sai dai ya yi abin kunya saboda kwallo bakwai kacal ya zura a wasa 76.

Hazard ya soma taka leda a kungiyar Lille inda ya ci kwallo 50 a cikin wasa 149 har ya lashe kofi biyu na Ligue 1 da Coupe de France a shekara ta 2011.

Ya koma Chelsea a 2012 a kan fam miliyan 32, kuma tauraruwarsa ta haska sosai a tsawon lokacinsa.

Hazard ya ci kwallo 110 a wasa 352 a Chelsea.

Karin labarai da za ku so karantawa: