Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man City na harin Branthwaite, United na son Neves da Faye
Manchester City na sa ido a kan babban danbayan Everton Jarrad Branthwaite, kuma Manchester United, da Tottenham, da ma Real Madrid duk suna son matashin na Ingila mai shekara 21. (Mail)
Yayin da wasu bayanai ke nuna cewa Manchester United na son sayar da danwasanta na tsakiya Scott McTominay, kungiyar na shirin rike danwasan na Scotland har ma ta kara girman kwantiraginsa. (Star)
Manchester United na harin sayen danwasan tsakiya na Benfica da Portugal Joao Neves, mai shekara 19, a matsayin daya daga cikin wadanda ta fi son saye a bazara. To amma kuma kungiyar kila ta fi mayar da hankali a kan Adrien Rabiot danwasan tawagar Faransa da ke Juventus kasancewar wanda za ta fi iya samu. (Caught Offside)
West Ham na shirin zawarcin danwasan Brentford da Ingila, Ivan Toney, mai kai hari, wanda kuma ake dangantawa da Arsenal da Chelsea. (Football Insider)
A mako mai zuwa Bayern Munich na son sanin matsayar danwasan baya na Canada Alphonso Davies a kan ko danwasan mai shekara 23 da ake dangantawa da Real Madrid, zai yarda ya kulla sabuwar yarjejeniya da Madrid din. (Sky Sports)
Tottenham na shirin tayin wuri na bazara wanda zai kai tsakanin fam miliyan 30 zuwa 40 a kan dan wasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher, wanda kwantiraginsa zai kare da Chelsea a 2025. (Football Insider)
Tottenham na nazari a kan danwasan gaba na Genoa Albert Gudmundsson kuma Inter Milan ma na sha'awar danwasan na tawagar Iceland mai shekara. (Football Transfers)
To amma Gudmundsson zai fi son tsayawa a Italiya kuma ma ya fi son zuwa Inter, kodayake Juventus ma na sa ido a kansa. (La Gazzetta dello Sport)
Julian Nagelsmann, mai shekara 36, ya ce ba ta yadda zai tsawaita kwantiraginsa a matsayin kociyan tawagar Jamsu har zuwa bayan gasar kasashen Turai ta bana wato Euro 2024, inda aka ce an yi tattaunawar ba shi sabon kwantiragi. (Metro)
Rui Pedro Braz na Benfica na gaba-gaba a jerin wadanda ake ganin za su gaji Dan Ashworth a matsayin darektan wasanni na Newcastle United. (Times )
Kila Manchester United ta nemi sayen matashin danbayan Senegal Mikayil Faye mai shekara 19 daga Barcelona, a bazara. (Mail)