Hikayata 2022: Mata uku da labaransu suka ciri tuta a gasar

Tuni dai alkalan gasar kagaggun rubutu ta mata zalla ta Hikayata suka zabi labarai guda uku da suka cancanci lashe gasar ta bana daga cikin 15 din da aka gabatar musu, bayan tafka muhawara.
Labaran guda uku dai su ne 'Haihuwar Guzuma' na Hassana Labaran Ɗanlarabawa daga birnin Kano da ke Najeriya da 'Gudun Gara' na Amira Souley daga birnin Maradi a jamhuriyar Nijar da kuma labarin 'Al’ummata' da Maryam Muhammad Sani ta rubuta daga birnin Kanon Najeriya.
A ranar Alhamis mai zuwa ne wato 03 ga watan Nuwamba za a yi gagarumin biki inda za a sanar da labarin da ya zamo na daya da na biyu da kuma na uku.
BBC za ta karrama wadanda suka zamo na daya da biyu da uku din da kudi da shaida da kuma lambar yabo, a karo na bakwai na bikin karrama wadanda labarin nasu ya ciri tuta.
Da ma dai an gabatarwa da alkalan labarai 25, inda suka zabi 15 sannan daga bisani suka tantance guda uku da su ne suka ciri tuta.
Duk da cewa labarai guda uku ne kawai za su samu kyautar kudi da lambar yabo, sauran labaran 12 za su samu shaidar yabo kawai sannan za a wallafa da karanta su a rediyo ta intanet.
Labarai 3 da suka ciri tuta:
- Al’ummata
- Haihuwar Guzuma
- Gudun Gara
Labarai 12 da suka cancanci yabo:
- Tsoro
- Na Tuba
- Komai Nisan Jifa
- A Dalilin ASUU
- Jarabta
- ‘Yancina
- Jarumar Mace
- Mai Kyau
- Nakasa Ba Kasawa Ba Ne
- Siyasarmu Ce
- Wannan Rayuwa
- Kaikayi












