Matar da ke taimaka wa mata mantawa da zafin cin amanar da aka yi musu

Asalin hoton, Somsara Rielly
- Shafin Google ya ce binciken da ake kan "yadda za a manta da cin amana" ya ƙaru cikin shekara biyar da ta gabata sannan ya ƙaru da ninki uku tun 2012
- KeywordTool.io, wata manhaja da ke ƙiyasta yawan kalmomin da ake dubawa a kafofi da dama , ta nuna cewa a Ireland an fi duba "yadda ake mantawa da cin amana" cikin shekara 10 da ta gabata sannan Najeriya da Singapore da India da Australiya da Kenya da Amurka da Burtaniya na daga cikin kasashen da ke gaba-gaba.
- A Tiktok, maudu'in #breakup ya bayyana fiye da sau biliyan 21 yayin da #getoverabreakup yake da miliyan 8.7
- Hukumar bayar da shawarwarin gyara kanka, ta ce sana'ar ba da shawara kan alaƙar mutum biyu, wadda ta shafi cin amana, a yanzu darajarta ta kai fiye da dala biliyan daya kowace shekara
Batun "batawa" na cikin batutuwan da suka karade shafin Tiktok inda kalmar da ta bayyana fiye da sau biliyan 21 ke nuna yadda mutane da dama ke son yin magana kan batun ko ma suke neman shawara kan cin amana.
A don haka, watakila, ba abin mamaki ba ne da ake samun masu bayar da shawara kan cin amana, kamar Aronke Omame, wadda take taimaka wa mutanen da suka fuskanci wannan yanayi.
Cikin 1993 sananniyar lauya Aronke Omame mai shekara 35 tana shirin koyar wani darasi kan cin amana da zai sauya rayuwarta.
Tana cikin wata kotu a Legas da ke Najeriya amma a karon farko, ba tsayawa wani abokin huldarta take ba.
Tana taimakon Mary, wata kawarta (ba sunanta na gaskiya ba), wadda iyayenta suka rabu.
Mahaifiyar Mary, a cewar Aronke, ta ci gaba da kallon mahaifin Mary da ke daya gefen.
Tana ta miƙa wuya domin janyo hankalinsa.
Sai kuma a lokacin da alkali ya nemi a yi gajeren hutu, Aronke na ci gaba da kallo a ƙame yayin da Mary da mahaifiyarta ke dosowa wajen mahaifin Mary.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kotun ta yi tsit, ana binsu da kallo. Akwai abin mamaki a abin da ya faru a gaba. Mary da mahaifiyarta sun durƙusa gaban mahaifinta.
Kansu a duƙe suna neman kada ya raba kan iyalin. Amma mahaifin Mary ya ɗaga haɓarsa yana mai yatsine baki ya fara jefa kalamai masu zafi yana ɗaga murya, a gaban kowa.
A Shekarar 1967 lokacin da Aronke ƴar shekara tara ke wasa a a fili tare da ƙawayenta lokacin da shugabar makarantarsu ta kusanto ta.
Ba kasafai ake ganin shugabar makaranta a wajen wasan yara ba.
Da walakin goro a miya. Ta faɗa wa Aronke cewa mahaifinta yana jiranta a bakin kofar makaranta.
Ya zo daukarta. Wani abin ya faru. Mahaifin Aronke ya fada mata cewa ba za su koma gida ba, za ta riƙa zama a gidan kakarta zuwa wasu ƴan makonni.
Kasancewar gidan kakarta na da nisa daga gari, babu wanda zai iya kai ta makaranta.
Ba za ta riƙa zuwa makaranta ba, kamar yadda mahaifinta ya sanar da ita.
Shi da mahaifiyarta za su riƙa leƙawa domin ganinta amma zuwa yanzu akwai abin da yake son su tattauna tsakaninsu.
Yana buƙatar su keɓe. Ta rasa inda mahaifinta ya dosa amma dai tana ganin yanzu ne lokacin da ya dace ta jefa masa tambayoyi.
Cikin ƴan makonni da ke tafe, aka ware ɗakuna ga Aronke da ƴan uwanta a gidan kakarta nesa daga hayaniyar jama'a yayin da mahaifiyarta da babanta suka iso domin tattaunawa da sauran dangi.
Suna barin ƴaƴansu a wajen kakanninsu kowace yamma, su kuma sai su koma gida. Gidan da ke fuskantar ɓaraka.

Asalin hoton, Somsara Rielly
Aronke tana wasa da ƴan uwanta kuma tana girki tare da kakarta.
Tana murna kaancewar ba za ta riƙa zuwa makaranta ba na wasu makonni. Aronke ta faɗa wa BBC cewa ta taso a hannun kakanninta da gwaggonta da kawunta.
Iyayena sun nemi taimako sosai. "Mahaifinta ya fice daga gidan mahaifansa ita kuma Aronke da ƴan uwanta sun koma.
Iyayenta suna da kusanci da juna kuma ba sa ƙalubalantar juna a gaban ƴaƴan.
Ba a samu ɓaraka ba. Kawai dai an rasa mutum ɗaya da yake kwana a gidan.
"Na fahimci cewa alaƙa ba ta cika yin ƙarko ba," Aronke ta bayyana cewa "duk da irin yaƙinin kowa.
"Abu ne mara daɗi a yi zaman doya da manja amma kawo karshen abu cikin mutunci zai fi martaba a gaba."
Ba ta fahimci dalilin da ya sa iyayenta suka rabu ba amma ba abin damuwa ba ne.
A cewarta, ta kasance cikin farinciki har ta girma. Amma darasin da ta koya a soyayya zai sosa rai.

Asalin hoton, SOMSARA RIELLY
Yanzu shekarar Aronke18 kuma tana makarantar koyon aikin lauya.
Ta faɗa soyayya da abokinta. Ajinsu ɗaya. Yadda suke tafiyar da rayuwarsu na daɗa masu armashi, lamarin da ya juye ya zama soyayya.
Aronke ta faɗa kogin soyayya karon farko. Amma akwai matsala. Yana son ya keɓe da ita, ita kuma ba ta shirya ba.
"Ban yadda da keɓewa kafin aure ba," a cewarta. Ta yi koƙarin ta faranta masa ta wasu bangarorin, kasancewa ta da shi, nuna masa kulawa.
Kwatsam wata rana, sai ta kai masa ziyarar ba-zata a gidansa, sai kawai ta ga masoyin nata tare da wata.
"Zuciyata ta yi rauni. Cikin fushi tana tunani cikin ranta cewa zai bi sawunta." Amma bai yi hakan ba.
End of Ƙarin Labarai masu alaƙa
Bayan shiru na kwanaki, sai ga wata wasiƙa. "Ya ce ya haɗu da wadda yake so, cewa ba ni da waje a zuciyarsa."
"Hakan ya matuƙar jefa Aronke cikin mummunan yanayin ƙunci.
"Na ji kunya. Na ji kamar rayuwata ta zo ƙarshe. "Ta shafe mako biyu ba ta zuwa makaranta.
Kullum tana maƙale a ɗaki tana shan kuka. Tana fargabar sake haɗuwa da shi.
Ta koma zaman gida. Ƙawayenta suna zuwa duba ta. Suna sanar da ita cewa kakarta ba ta yanke saƙa ba - akwai waɗanda suka fi shi.
Sai wata rana, kamar a mafarki, sai ta samu ƙwarin gwiwa. Ta ji tana son fita. Karatunta na digiri na jiranta da kuma ƙawayenta da za su shaƙata.
Sai ta fita waje, rayuwarta ta dawo dai-dai. Makonni biyun da ta shafe a gida sun taimaka mata matuƙa.
A wani lokacin ta ma ji kamar za ta iya sake zama a matsayin ƙawarsa. "Na ji sanyi da na zub da hawaye," a cewarta, "Darasi ne babba. Na zub da hawaye."

Asalin hoton, Somsara Rielly
A lokacin da shekarunta suka kai 17, cikin wata kotu a Legas, Aronke na kallo cikin tsoro dai-dai lokacin da mahaifin Mary ke jefa wa matarsa da ƴarsa da ke tsugune kan gwiwoyinsu magana.
Yana ta jefa maganganu da ba zan iya tuna su ba. Na share su daga zuciyata," Aronke ta ƙara da cewa "amma kalaman sam babu daɗin ji."
"Ba a ɗauki lokaci ba, aurenta ya mutu, amma nata bai yi munin irin baƙaƙen maganganun da jama'a suka fada ba.
Ta yi mamakin yadda mace yar shekara 60 za ta iya durƙusa wa namiji wanda yake wulaƙanta ta, sannan ta roƙe shi kada ya rabu da ita.
Sai na raya wani abu a rai. "Tsarin taimaka wa matan da mazajensu ke cin zarafinsu," Aronke ta ce.
"Ko da ban yi tunanin haka ba a baya, yanzu na yi."












