Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan manufofi bakwai na dan takarar Labour Party Peter Obi
A Najeriya, yayin da ake fuskantar babban zaɓen ƙasar 'yan takarar shugabancin ƙasar na ci gaba baje-kolin manufofin yaƙin neman zaɓensu da nufin jan hankalun 'yan ƙasar wajen kaɗa musu ƙuri'a a babban zaɓen da ke tafe.
Hukumar zaɓen ƙasar dai ta saka ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasar.
'Yan takara 18 ne dai za su fafata a zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe, fitattu daga cikinsu sun haɗar da Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC, da Peter Obi na jam'iyyar Labour da Dr Rabi’u Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, da Atuku Abubakar na jam'iyyar PDP.
Kamar sauran takwarorinsa 'yan takara, shi ma ɗan takarar shugaban ƙasar ƙarƙashin jam'iyyar Labour Peter Obi ya bayyana nasa manufofin da ya ce zai mayar da hankali a kansu da zarar ya samu nasarar ɗarewa shugabanicn ƙasar.
Mista Obi ya bayyana ƙudurorin nasa mai shafi 72 a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi da safe.
Wanda ya yi wa take da ''Abu ne mai yiyuwa: Yarjejeniyarmu da 'yan Najeriya'
Cikin ƙudurorin nasa, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya lissafo batutuwa bakwai da ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kansu.
Ciki har da batun kawo gagarumin sauyi a fannin shari'a ta yadda doka za ta yi aiki a kan kowa.
Ga abubuwa bakwai da ya alƙawarta mayar da hankali a kansu idan an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar a zaɓen na baɗi da ke tafe.
Kawo ƙarshen Ta'addanci
Ya bayyana cewa zai ceto Najeriya, ta hanyar kawo ƙarshen ayyukan 'yan fashin daji da masu tayar da ƙayar baya.
Ya ce zai ɗauki matakai domin samar da haɗin kai tsakanin ƙasashen makwabta musamman ƙasashen Nijar da Chadi da Kamaru da nufin magance matsalar tsaro a kan iyakokin ƙasar.
Ɗan takarar ya ce zai yi ƙoƙari wajen kawo haɗin kai tsakanin 'yan ƙasar mabiya addinai da ƙabilu daban-daban, ta yadda babu wanda za a bari a baya.
Bunƙasa tattalin arziki
Ɗan takarar ya ce zai mayar da hankali wajen samar da manyan masana'antu domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasar da yadda za a riƙa fitar da abubuwa masu yawa zuwa ƙasashen ƙetare.
Ya ce zai ɓullo da sabbin manufofi game da tattalin arziki ta yadda ƙasar za ta samu sukunin rage basussukan da ake binta.
Domin magance matsalar ƙaranci da tsadar abinci a ƙasar, ɗan takarar ya ce zai kawo gagarumin sauyi tare da ɓullo da sabbin tsare-tsaren noma da zuba jari a ɓangaren noma a fadin jihohin ƙasar 36 da Abuja babban birnin ƙasar.
Tabbatar da ƙarfin doka
Mista Obi ya ce zai kawo sauyi a ɓangaren shari'ar ƙasar ta yadda zai tabbatar da cewa doka ta yi aiki a kan kowa.
Musamman wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.
Sannan ya ce gwamnatinsa za ta rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa, tare da tabbatar dacewa ma'aikatan gwamnati na aikinsu yadda ya kamata
Kimiyya da fasaha
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce zai ɗora ƙasar kan turbar amfani da masana'antu na zamani ta hanyar amfani da kimiyya da fasahar zamani domin inganta tattalin arzikin kasar.
Ya ce zai tabbatar da matasa sun sami horo a fannin fasahar zamani ta yadda za su amfanar da kawunansu ta hanyar samun sana'o'in da za su dogara da kansu.
Ababen more rayuwa
Ɗan takarar na jam'iyyar Labour ya ce zai gina manya-manyan ababen more rayuwa domin samar da dawwamammiyar wutar lantarki, da bunƙasa sufurin jiragen ƙasa da na sama da kuma gyara titunan mota.
Ya ce zai saka hannu kan sabuwar dokar kafa ma'aikatar sufuri ta ƙasa - 'National Transport Commission' - wadda 'yan majalisa suka amince da ita tun a shekarar 2018.
Tallafin karatu ga matasa
Domin matasan ƙasar su sami ilimi ta yadda za su yi gogayya da takwarorinsu na ƙasashen duniya, ɗan takarar ya ce zai samar da wani tsari da za a riƙa bayar da tallafin karatu da na bincike, a fannonin lafiya da na kasuwanci.
Haka kuma ya ce zai ɓullo da tsarin wajibcin karatu ga 'kowanne yaro' a ƙasar.
Kyautata dangantaka da ƙasashen duniya
Ɗan takarar ya ce zai samar da kyakkyawar huldar dangantaka tsakanin Najeriya da ƙasashen duniya domin kare mutunci da yancin 'yan ƙasar mazauna ƙetare.
Sannan kuma ya alƙawarta bunƙasa kasuwan Najeriya da na 'yan ƙasar a idanun duniya.
A 'yan kwanakin baya-bayan nan dai ɗan takarar na fuskantar suka kan rashin bayyana manufofin nasa, musamman daga jam'iyyun hamayya.
A watan Okbota Mista Obi ya nesanta kansa daga wasu manufofi da aka danganta shi da su.
Inda ya ce zai bayyana manufofin nasa ga al'umma da zarar sun kammala.