Masu ninƙaya da masu rawa a cikin hotunan Afirka na wannan mako

DANIEL BELOUMOU OLOMO/ AFP

Asalin hoton, DANIEL BELOUMOU OLOMO/ AFP

Bayanan hoto, Nan, masu rawa ne ke shirin cashewa a wani bikin al'adu da aka gudanar a birnin Douala na ƙasar Kamaru a ranar Asabar domin karfafa haɗin-kan ƙasa.
An wallafa
IHSAAN HAFFEJEE

Asalin hoton, IHSAAN HAFFEJEE/ GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Wannan kuma wata ƴar wasan rawa ke cashewa a wani wuri da aka sanya wa sunan Nelson Mandela, jigo a yaki da wariyar launin fata da kuma haɗin-kai, da aka gudanar a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.
In Eritrea, camel riders are seen on Tuesday in Gash-Barka region as they gear up for Independence Day on 24 May in the one-party state.

Asalin hoton, SHABAIT.COM

Bayanan hoto, Nan wasu ma-haya dawaki ne a Eritrea ke shiri a lardin Gash-Barka gabanin bikin ranar samun ƴancin kan ƙasar da za a yi a ranar 24 ga watan Mayu.
KHALED ELFIQI

Asalin hoton, KHALED ELFIQI/ EPA

Bayanan hoto, A birnin Giza na ƙasar Masar kuwa, batun kayan ƙawa ake, inda nan wani mai tallata kayan ƙawa Waseem Khadra ya gabatar da wani kaya da ya kirkiro.
KHALED ELFIQI

Asalin hoton, KHALED ELFIQI/ EPA

Bayanan hoto, Sama da masu kayan ƙawa 70 ne suka baje-kolin kayakinsu a wani bikin tallata kayan ƙawa irinsa na farko da aka gudanar a Masar.
FADEL DAWOD

Asalin hoton, FADEL DAWOD/ GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A can Port Said kuwa, Mohamed Ghaly yana ta ƙoƙarin ƙera garaya.
STEFANO RELLANDINI

Asalin hoton, STEFANO RELLANDINI/ AFP

Bayanan hoto, Ɗan ƙasar Mali Souleymane Cissé, wanda ake ɗauka a matsayin ɗaya daga cikin fitattun masu shirya fina-finai na Afirka a tarihi, ya tsaya a gabar tekun Cannes na ƙasar Faransa a ranar Talata domin ɗaukar hoto.
ANTONIN THUILLIER

Asalin hoton, ANTONIN THUILLIER/ AFP

Bayanan hoto, Nan, lokaci ne da 'yar wasan fim na kudancin Najeriya Chika Ike ke isa wurin bikin buɗe bikin fina-finan Cannes da ake gudanarwa kowace shekara a birnin na Faransa.
ISSOUF SANOGO

Asalin hoton, ISSOUF SANOGO/ AFP

Bayanan hoto, Marubuciyar ƙasar Ivory Coast Marguerithe Abouet ta baje kolin littafinta na barkwanci a bikin baje kolin litattafai na ƙasa da ƙasa na Abidjan a ranar Asabar.
NIC BOTHMA

Asalin hoton, NIC BOTHMA/ REUTERS

Bayanan hoto, Duk dai a ranar a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu, waɗannan mata sun nuna damuwarsu game da sauyin yanayi a wata zanga-zangar da suka yi gabanin ranar iyaye mata.
HASSAN ALI ELMI

Asalin hoton, HASSAN ALI ELMI/ AFP

Bayanan hoto, Da alama sauyin yanayi ya yi nisa da tunanin wannan matashi yayin da ya nutse cikin ruwa a birnin Beledweyne na Somaliya a ranar Lahadin da ta gabata.
HASSAN ALI ELMI

Asalin hoton, HASSAN ALI ELMI/ AFP

Bayanan hoto, Nan kuma, lokaci ne da kogin Shabelle a ƙasar Habasha ya malalo ruwa tare da yashe kayayyaki