Chelsea ta ɗauki mai tsaron raga Jorgensen daga Villareal

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta ta kammala ɗaukar golan Villarreal, Filip Jorgensen kan fan miliyan 20.7 kan ƙwantiragin shekara bakwai.
Dan wasan tawagar Denmark, mai shekara 22, ya buga wa Villarreal wasa 37 a kakar da ta wuce, bayan da ya zama mai tsaron ragar da kungiyar ke amfani da shi.
"Wannan matakin mafarki na ne ya zama gaske," in ji Jorgensen. "Na yi matukar farin ciki da komawa Chelsea, ɗaya daga cikin manyan kungiyoyin tamaula a duniya.
Ana sa ran Jorgensen zai kalubalanci gola, Robert Sanchez a matsayin wanda zai ke fara tsare ragar Chelsea.
An haife Jorgensen a Sweden, ya wakilci ƙasar a matakin matashi daga baya ya koma Denmark kasar mahaifinsa, inda ya fara daga matasa ƴan kasa da shekara 21.
Ya rattaba hannu a Villarreal tun yana ɗan shekara 15 daga nan ya sa kwazo har zuwa manyan ƴan wasan ƙungiyar da fara taka leda a Oktoba 2020.
Jorgensen, wanda ya fara buga gasar La Liga a watan Janairun 2023, ya je Amurka, inda Chelsea ke atisayen tunkarar kakar bana.
Sauran wasa uku ke gaban Chelsea a Amurka, wadda za ta kara da Club America da Manchester City da Real Madrid, watakila a gwada Jorgensen a lokacin.
A ranar Lahadi 18 ga watan Agusta ne Chelsea za ta fara gasar cin kofin Premier da Manchester City.











