'Ɗaurin shekara 14 ne hukuncin masu digirin bogi ɗan Kwatano'

Cotonou gate

Asalin hoton, DailyNigerian

An wallafa

Masana harkar shari'a sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da badakalar takardun shaidar kammala digiri daga jami'o'i, a kasar Benin.

A farkon makon nan ne dai jaridar DailyNigerian ta wallafa labarin ma'aikacinta da ya yi bad-da-bami ya yi bincike na kwakwaf dangane da badakalar.

A wani martani na gaggawa kuma gwamnatin Najeriya ta dakatar da amincewa da duk wani kwalin karatun digiri daga kasashen Benin da Togo.

Wannan batun dai na ci gaba da jan hankalin 'yan Najeriya ciki da wajen kasar, inda suke ta kiraye-kirayen cewa ya kamata gwamnati ta zurfafa bincike domin bankado tushen badakalar.

Tuni dai hukumar ICPC da ke yaki da almundahana a Najeriya, ta ce ta fara bincike game da badakalar.

To sai dai masana irinsu Barrister Bulama Bukarti na ganin ya kamata binciken ya shafi hukumomi da dama na gwamnati.

Sai dai kuma ya ce akwai bukatar a tantance wadanda suka yi halastaccen digiri sabanin na bogi.

Dangane kuma da hukuncin da ya dace da masu irin wannan digiri na boge, Barrister Bukarti ya ce akwai tanade-tanaden a kundin tsarin mulkin Najeriya.

"Tsarin dokokin Najeriya ya tanadi daurin shekara 14 ga duk wanda ya mika takardar karatu ta bogi, sannan kuma akwai tanadin daurin shekara biyu ga wanda ya mika irin wannan shaida ga hukumar yi wa kasa hidima." In ji Bukarti.

Bayanan sautiDaurin shekara 14 ne hukuncin masu digiri dan kwatano na boge - Bukarti.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shi ma Dr Aliyu Tilde kwararre a fagen Ilimi, ya ce matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka kan batun ya yi daidai, amma abin lura shi ne ba kowanne digiri da aka samu daga kasashe kamar Benin ko Togo, ko Kenya ko Uganda ne marasa inganci ba.

Ya ce ''suna da makarantu masu kyau da inganci da sun fi na Najeriya ma, kuma ba lallai ne dan Najeriya da ke neman shiga irinsu ba lallai ya samu ba''

Dakta Tilde ya ce ''Abin da ke sanya daliban Najeriya zuwa kasashen waje don karatu sun hadar da raguwar ingancin jami'o'in Najeriya, da yawan yajin aiki, da batun jarrabawar shiga jami'a wato Jamb, sai kuma halin da'a da ake tilastawa musamman 'yan mata, wadannan ne manyan dalilai''.

Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya ya kamata ta yi kyakkyawan bincike da tantance jami'o'in da ake da su a cikin gida.

''A lokacin da muka hau mulki a shekarar 2019, a jihar Bauchi mun samu kwalejojin ilimi sama da 50, da muka zauna muka yi aikin tantance su, sai muka lura ba su fi 10 ne kadai masu inganci ba.

''Dan haka gwamnatin jiha ta ba da umarnin rufe su, kuma an yi hakan, irin wannan matakin ya kamata gwamnatin Najeriya ta dauka.''

Wasu dai na ganin akwai sakacin gwamnati na wanzuwar irin wadannan jami'o'i ko kwalejojin ilimi.

Kuma Tilde ya ce an san da zaman wadannan makarantu tun daga kan jami'an gwamnati dan haka yanzu ba lokacin tashin tashina ba ne, a maida hankali wajen tunkarar matsalar da yadda za a magance ta da kauce wa aukuwar hakan nan gaba.

A karshe ya ce abin da ya rage shi ne daliban da suka yi irin digirin su san yadda za su fidda kansu, gwamnati ta rufe su, ta kuma zama gatan talaka a kuma daina yaudarar iyaye kan hakan.