Man City ta koma ta huɗu a teburin Premier League

Man City

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City ta doke Crystal Palace da cin 5-2 a wasan mako na 32 a Premier League da suka buga ranar Asabar a Etihad.

Palace ce ta fara cin biyu cikin minti 21 da fara tamaula ta hannun Eze da kuma Richards, ta kuma zura na uku a raga, amma aka soke da cewar an yi satar gida.

Daga nan Manchester City ta saka kaimi ta zura biyar a raga ta hannun Kevin de Bruyne da Omar Marmoush da Mateo Kovacic da James McAtee da kuma Nico O'Reilly.

Wannan shi ne karo na 63 da City ta ci ƙwallo biyar a wasa a Premier League, inda daga 39 a karkashin Pep Guardiola aka zazzaga a raga.

Da wannan sakamakon City ta koma mataki na huɗu a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki uku tsakani da Nottingham Forest ta uku.

Ranar ta Asabar Forest za ta fafara da Everton a wasan mako na 32 a Premier League a City Ground.

A kaka mai zuwa a Champions League, ƙungiya biyar ce za ta wakilci Ingila, kenan daga matakin farko a teburin Premier zuwa na biyar.

Watakila a Ingila a samu ƙungiya shida ta wakilci kasar a Champions League, idan Manchester United ko Tottenham ta lashe Europa League.

Man City za ta je Everton a wasan mako na 33 a Premier League ranar 19 ga watan Afirilu, sannan City ta kara da Aston Villa ranar Talata 22 ga watan Afirilu a Etihad.