Marciniak ne zai busa wasan Atletico da Real a Champions League

Szymon Marciniak

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon kafa ta nahiyar Turai, Uefa ta bayyana Szymon Marciniak a matakin wanda zai busa wasan Real da Atletico a Champions League ranar Laraba.

Atletico za ta karɓi bakuncin Real a wasa na biyu zagayen ƴan 16 a gasar zakarun Turai, inda Real ta yi nasara 2-1 ranar Talata a Santiago Bernabeu.

Marciniak dan kasar Poland zai yi alkalancin wasan da ya shafi Real Madrid a karo na tara a tarihi.

Wasan da Marciniak ya yi alkalancin Real Madrid a Champions League:

  • Atalanta-Real Madrid (2-3). Wasa na shida 2024-25
  • Real Madrid-Bayern Munich (2-1). Daf da karshe zagaye na biyu 2023-24.
  • Manchester City-Real Madrid (4-0). Daf da karshe zagaye na biyu 2022-23.
  • Real Madrid-Chelsea (2-3). Kwata fainal zagaye na biyu 2021-22.
  • Sheriff-Real Madrid (0-3). Wasannin cikin rukuni 2021-22.
  • Real Madrid-Tottenham (1-1). Wasannin cikin rukuni 2017-18.
  • Real Madrid-Borussia Dortmund (2-2). Wasannin cikin rukuni 2016-17.
  • Real Madrid-Roma (2-0). Zagayen ƴan 16 zagaye na biyu 2015-16.

A Uefa Super Cup:

9. Real Madrid-Atlético (2-4) a shekarar 2018-19.