Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa na kara yin tsauri a Man City - Guardiola
Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya ce abubuwa na kara yin tsauri a wasannin da suke yi a kakar bana.
Ranar Asabar, City mai rike da Premier League ta yi rashin nasara 2-1 a gidan Bournemouth, kafin nan aka yi waje da ita a Carabao Cup a hannun Tottenham 2-1.
Karon farko da aka ci City a Premier League, wadda ta yi wasa 32 a jere ba tare da an doke ta ba a babbar gasar tamaula ta Ingila.
To sai dai City za ta fuskanci Sporting a Champions League ranar Talata, kenan zai fafata da Ruben Amorim, wanda Manchester United ta ɗauka madadin Ten Hag.
City tana fama da fitattun ƴan wasanta da ke jinya, ciki har da Rodri tun daga watan Satumba, wanda gama wasannin kakar nan - shi ne ya lashe ƙyautar Ballon d'Or ta bana.
Guardiola ya ce City tana tsaka mai wuya a bana, bayan da take fama da ƴan wasa da ke jinya da ya haɗa da John Stones da Ruben Dias da kuma Kevin de Bruyne.
City tana mataki na biyu a teburin Premier League da maki 23 da tazarar maki biyu tsakani da Liverpool mai jan ragama, bayan karawar mako na 10.
Da zarar City ta kammala Champions League da Sporting ranar Talata, za ta je gidan Brighton ranar Asabar, domin buga Premier League.
Daga nan City za ta kara fuskantar Tottenham a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Asabar 23 ga watan Nuwamba a Etihad.