Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chiesa yana cikin ƴan Liverpool a karawa da AC Milan
Federico Chiesa yana cikin ƴan wasan Liverpool da suka je AC Milan a wasan farko a cikin rukuni a Champions League da za su kara a San Siro ranar Talata.
Chiesa mai shekara 26, ya koma ƙungiyar Anfield kan fara kakar bana daga Juventus kan £10m cikin Agusta, koda yake har yanzu bai buga wasa ba.
Liverpool, wadda ta kara a Europa League a bara za ta buga Champions League a bana, karon farko bayan kaka ɗaya tsakani.
Liverpool, wadda ta fara lashe wasa uku da fara kakar bana a Premier League ta yi rashin nasara 1-0 a Anfield a hannun Nottingham Forest ranar Asabar.
Kawo yanzu ba wani ɗan wasa daga Liverpool da ya ji rauni, kenan ta je Italiya da kwarin gwiwa.
Haka kuma Liverpool ta je da Tyler Morton birnin Milan daga ƴan wasa 23 da ta bayyana, mai shekara 21 ya buga wasannin aro a bara a Hull City.
Ƴan wasan Liverpool da aka je da su Milan:
Alisson, Gomez, Endo, Van Dijk, Konate, Diaz, Szoboszlai, Nunez, Mac Allister, Salah, Chiesa, Jones, Gakpo, Jota, Tsimikas, Robertson, Gravenberch, Jaros, Kelleher, Alexander-Arnold, Quansah, Morton da kuma Bradley.
Wasannin da aka buga tsakanin ƙungiyoyin biyu a Champions League:
2021/2022
Champions League Talata 7 ga Disambar 2021
- Milan 1 - 2 Liverpool
Champions League Laraba 15 ga Satumbar 2021
- Liverpool 3 - 2 Milan
2006/2007
Champions League Laraba 23 ga watan Mayun 2007
- Milan 2 - 1 Liverpool
2004/2005
Champions League Laraba 25 ga watan Mayun 2005
- Milan 3 - 3 Liverpool