Mutum 51 sun mutu a wata fashewa a wurin haƙar ma'adinai a Iran

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Fashewar tukunyar iskar gas a wurin haƙar ma'adinai a gabashin Iran ta kashe mutane aƙalla 51, kamar yadda kafar yaɗa labaran ƙasar ta bayyana a ranar Lahadi.

Fiye da wasu 20 ne kuma suka jikkata bayan fashewar a lardin Khorasan ta Kudu.

An ruwaito cewa fashewar ta sinadarin methane ta afku a wasu sassa biyu na wurin haƙar ma'adinan a garin Tabas mai tazarar kilomita 540 a kudu maso gabashin Tehran, babban birnin ƙasar.

Fashewar ta afku ne da misalin karfe 9:00 agogon ƙasar a ranar Asabar, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka bayyana.

Gwamnan Kudancin Khorasan, Javad Ghenaatzadeh ya ce akwai ma'aikata 69 a wurin lokacin da aka samu fashewar.

Kamfanin dillancin labarai na AP, ya ce: “An samu fashewar wani abu kuma abin takaici mutum 69 ne ke aiki a wurin haƙar ma’adinan a Madanjoo.

"Akwai mutane 22 a sashe na farko na wurin, sannan mutum 47 a ɗaya sassan."

Har yanzu dai ba a san adadin mutanen da suka rage a raye ba da kuma waɗanda suka maƙale a wurin haƙar.

Yanzu kafofin yaɗa labaran ƙasar sun sake sabunta alkaluman waɗanda suka mutu a farko wanda suka ce ya kai 30.

Kamfanin dillancin labarai na IRNA ya bayar da rahoton cewa, adadin ma'aikatan da suka mutu ya ƙaru zuwa 51, sannan adadin waɗanda suka jikkata kuma ya ƙaru zuwa 20.

Kafar talabijin ta ƙasar Iran ta ruwaito shugaban hukumar bayar da agaji na Red Crescent na cewa mutum 24 ne suka ɓata kawo yanzu.

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya miƙa sakon ta'aziyya zuwa ga iyalan da suka rasa ƴan uwansu, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

"Na yi magana da ministoci kuma za mu yi iya ƙoƙari wajen bibiyar batun," in ji Pezeshkian a wani jawabi da aka watsa a gidajen talabijin na ƙasar.

Wurin hakar ma'adinan a Tabas yana da faɗin fili fiye da murabba'in kilomita 30,000 kuma tana da tarin sinadarin da ake amfani da su wajen yin girki, a cewar IRNA.

Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ambato mai gabatar da ƙara na ƙasar Ali Nesaei yana cewa "tarin iskar gas a wurin hakar ma'adinan" ya sanya wahala a aikin ceto.

"A halin yanzu, abin da muka saka a gaba shi ne bayar da agaji ga waɗanda suka jikkata da kuma fitar da mutane daga karkashin baraguzan ginin," in ji Nesaei.

Ya ƙara da cewa za a hukunta jami'an da suka yi sakaci har ta kai ga afkuwar lamarin.

A bara, fashewar wani abu a wurin hakar ma'adinin kwal a birnin Damghan da ke arewacinƙkasar, ya yi sanadiyar mutuwar mutum shida wanda kuma mai yiwuwa shi ma ya faru sakamakon tsiyayar sinadarin methane, a cewar kafofin yaɗa labaran ƙasar.

A watan Mayun 2021, wasu ma'aikatan haƙar ma'adinai biyu sun mutu a wata rugujewa.

Wata fashewa ma a 2017 ta kashe masu haƙar ma'adinai 43 a garin Azad Shahr da ke arewacin Iran, wanda ya janyo fushin jama'a zuwa ga hukumomin na Iran.