Ko Aston Villa za ta doke Juventus a Champions League?

Asalin hoton, Getty Images
Aston Villa - wadda ta yi wasa shida a jere ba tare da nasara ba - na shirin buga Champions League da Juventus a Villa Park ranar Laraba.
Sai dai kociya, Unai Emery bai faɗi dalilin da ba sa kokari ba, wanda bai yi maganar yawan wasanni da ƴan ƙwallo ke fuskanta da aka ce yana daga cikin dalili.
Rashin ƙoƙarin ƙungiyar a dukkan fafatawa ya sa an yi waje da ita a League Cup na bana, sannan ta yi kasa zuwa mataki na takwas a Premier League.
Haka kuma tana ta takwas a teburin Champions League mai ƙungiyoyi 36 a sabon fasalin da ake yi daga kakar nan.
Wannan shi ne karo na uku da za su fuskanci juna a gasar zakarun Turai tun bayan 1982/83, Inda Juventus ta yi nasara 5-2 gida da waje.
Wasan da aka kara tsakanin Aston Villa da Juventus
European Cup Laraba 16 ga watan Maris 1983
- Juventus 3 - 1 Aston Villa
European Cup Laraba 2 ga watan Maris 1983
- Aston Villa 1 - 2 Juventus
Sauran wasa tara a shiga sabuwar shekara, Villa za ta karɓi bakuncin Juventus, wadda ba a doke ta ba a Serie A kawo yanzu a kakar nan.
Juventus tana da tsauri a Serie A, wadda take da masu tsaron baya masu kyau, har ma Emery ya jinjina wa Thiago Motta, kan yadda yake ƙwazo a bana.
Villa tana fama da ƴan wasan da ke jinya kamar Amadou Onana da Jacob Ramsey, sai dai Emery ya ce Ezri Konsa da Boubacar Kamara sun murmure.
Onana ya yi zaman benci a wasan Villa da Crystal Palace da suka tashi 2-2 a Premier a ƙarshen mako, wanda ya ji rauni a wasa da Liverpool.











