Shin kun san shan ruwa ba daidai ba zai iya kashe mutum farat ɗaya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Busayo James-Olufade
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Muna matuƙar buƙatar shan ruwa don rayuwar yau da kullum da ma lafiyarmu, to amma idan muka sha ruwan da ya wuce kima muna iya sanya rayuwarmu cikin hatsarin wata cuta da ake kira 'Hyponatremia'.
Wata mata mai wasan tsalle-tsalle, Johanna Pakenham, ta kusa rasa ranta a 2018 bayan da ta sha ruwa lita biyar.
Cikin wata hira da ta yi da BBC, ta ce bata taba tunanin cewa ruwa zai iya kashe mutum ba.
Wata rana, Johanna na wasa sai ta sha ruwa lita biyar.
Anan ne sai aka ga ta yanke jiki ta fadi kasa anan ne aka dauke ta sai asibiti.
Koda aka kaita asibiti sai aka ce ruwan da ta sha ya janyo mata cutar Hyponatremia, wato cuta ce wadda ke afkuwa idan mutum ya sha da yawa.
Akwai wata mata mai suna Michelle Whitehead, da ta rasa ranta a watan Satumbar 2023, bayan ta sha ruwa mai yawa.
Matar mai 'ya'ya biyu ta kasance tana asibitin masu tabin hankali inda ake mata magani, anan ne ta sha ruwan daya wuce kima lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.
Yaushe shan ruwa ke haifar da hyponatremia?
Ƙwararru sun ce idan har mutum ya sha ruwa mai yawa a lokaci guda, misali bayan ya yi atisaye ko kuma bayan ya sha barasa mai yawa, to ruwan kan haddasa Hyponatremia.
Haka ma idan mutum na da cutuka kamar cutar koda, kodar ba ta iya tace ruwan da ba a bukata a cikin jiki, hakan kuma kan sa kodar mutum ta samu matsala saboda ruwan jikin mutum ya yi yawa.
Hanyar da ake bi wajen maganin cutar Hypotremia, ita ce ta yiwa mutum allurar da aka hadata da gishiri da wasu sinadarai.
Kuma yin wannan allurar na bawa koda damar fitar da ruwan da ba a bukata ajikin mutum sai mutum ya yi ta fitsari.
Ta yaya za a sha ruwan da ya kamata?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Adadin ruwan da ya kamata mutum ya sha, ya danganta ne ga kowanne irin mutum da kuma lafiyarsa da shekara da girma da irin aikin da ya ke yi dama a wanne waje yake rayuwa.
A 2010, hukumar kula da ingancin abinci ta Tarayyar Turai EFSA, ta ce wani bincike ya gano cewa shan ruwa lita daya ga mace yana da matukar kyau, maza kuma lita biyu da rabi shi ne dai-dai.
Masu bincike sun ce kashi 20 cikin 100 na ruwan da muke sha na zuw ne daga abincin da muke ci.
Kazalika kwararru sun ce yana da kyau mutum ya sha ruwa lita uku ko kuma kofin ruwa takwas a kowacce rana.
To amma wani sabon bincike da masana kimiyya a jami'ar Aberdeen ta yi a 2022, ya gano cewa ruwa lita biyu a jikin dan adam ma ya yi yawa a sha a rana guda.
Kwararrun sun ce akalla ana son mutum ya sha ruwa d abai wuce lita 1.8 ba a rana.
Farfesa John Speakman daga jami'ar Aberdeen, ya shaida wa BBC cewa, adadin ruwan daya kamata mutum ya sha na da bambanci da adadin ruwan da jikin mutum ke bukata d ama ruwan da muke samu daga abinci.
Ya ce, saboda mutane ba sa auna adadin ruwan da suke sha da wanda suke samu daga abinci, shi ya sa basu da tabbas akan ruwan da suke bukata a jikinsu.
Yaushe za mu san babu ruwa mai yawa a jikinmu?
Gaskiya ne shan ruwa mai yawa na janyo abubuwan da aka lissafa a farkon wannan makala, to amma idan har mutum ya sha ruwan da cikins aya cika makil to abin ya wuce kima.
Yana da kyau ka sha ruwa har sai ka daina jin kishirwa.
Ka guji shan ruwan da ya wuce kima ko shan duk wani abu mai ruwa-ruwa da yawa a lokaci guda.
A don haka a duk lokacin da ka ke son shan ruwa koda bayan ka gama atisaye, ko kuma shan barasa, ka tuna cewa idan ka sha da yawa zai iya maka illa.











