Yadda yaƙi ke ƙara ruruwa a Gabas ta Tsakiya

    • Marubuci, David Gritten
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Isra'ila ta ce ta ƙaddamar da farmaki ta ƙasa a kudancin Lebanon kan ƙungiyar Hezbollah, lamarin da ke ƙara rura rikicin da ke barazanar ɓarkewar yaƙi a yankin.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta sun kai farmaki a ƙauyuka kusa da kan iyaka, yayin da jiragen yaƙi ke ci gaba da luguden wuta a Lebanon.

Wannan ya biyo bayan illar da Isra'ila ta yi wa Hezbollah, ciki har da kisan shugabanta Hassan Nasrallah.

Duk da cewa an yi wa Hezbollah illa, amma ta jajirce. Ƙungiyar ta ci gaba da harba rokoki zuwa arewacin Isra'ila kuma ta ce a shirye take ta abka yaƙi.

Ga abin da muka sani kan abubuwan da ke faruwa.

Isra'ila ta fara mamayar Lebanon kusan shekaru 20

Wakilin BBC a Gabas ta Tsakiya Hugo Bachega Beirut ya ce Lebanon ta tashi ne da sabon labarin cewa Isra'ila ta ƙaddamar da farmaki ta ƙasa a kudanci.

Fargabar ita ce wannan zai iya zama babbar manufa ta yaƙar Hezbollah, da ta shafe wata tana yaƙi da Isra'ila a 2006.

A wata ƙaramar sanarwa a ranar Talata, rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa dakarunta tare da taimakon jiragebn yaƙi da makaman atilare sun fara kai farmaki kan Hezbollah a ƙauyukan da ke kan iyaka, tana mai cewa sun kasance barazana ga al'ummar Isra'ila da ke arewaci.

A cewar wakiliyar BBC a Gabas ta Tsakiya Lucy Williamson a arewacin Isra'ila, jirage masu saukar ungulu da ƙananan jirage sun yi tashawagi a kan iyaka cikin dare. Da safe kuma kusa da kan iyaka an jibge tankokin yaƙi.

Rundunar sojin ba ta bayyana yawan dakarun da ta jibge ba da kuma yadda za su doshi yankin Lebanon.

Sai dai wani babban jami'in tsaro ya shaida wa BBC cewa wannan ba "asalin yawansu dakarun ba ne da za su yi yaƙi ta ƙasa."

Amma tura dakaru ta ƙasa kusa da Lebanon yana tattare da hatsari. Hezbollah, da ke da tankokin yaƙi da masu kakkabo makamai masu linzame da nakiya, ta daɗe tana son gwabzawa da dakarun Isra'ila a wurin tsawon shekaru.

Hezbollah ta ce dakarunta a shirye suke

A ranar Talata, mai magana da yawun ƙungiyar Hezbollah Mohammed Afif ya musanta ikirarin cewa dakarun Isra'ila sun tsallaka kudancin Lebanon tare da cewa "babu wani faɗa da aka gwabza."

Amma ya ƙara da cewa ƙungiyar a "shirye take ta gwabza da dakarun maƙiya idan har suka taka ƙafarsu cikin Lebanon domin za su tafka mummunan hasara."

Hezbolla ta kuma harba rokoki da makamai masu linzami a Isra'ila - hare-haren da Mr Afif ya ce somin taɓi ne" kan martaninsu ga hare-haren Isra'ila.

An ta jin ƙarar gargaɗi a garin Metula da ke kan iyaka, inda Hezbollah ta ce dakarun sun kai wa dakarun Isra'ila hare-haren roka.

Ƙungiyar ta kuma yi iƙirarin cewa ta harba makamai masu linzami zuwa sansanonin Isra'ila na leƙen asiri a Tel Aviv. Jami'an lafiya sun ce mutum biyu suka ji rauni a babbar hanya kusa da Kafr Qasim.

Illar da aka yi wa Hezbollah

Isra'ila ta yi wa Hezbollah mummunar illa a makwannin da suka gabata, inda ta kashe gwamman kwamandojinta tare da lalata dubban makamai a hare-hare ta sama.

Editan BBC Jeremy Bowen ya ce babbar illa ita ce ta kisan Hassan Nasrallah a harin sama a Beirut a ranar Juma'a.

Fiye da shekara 30, shi ne jigon Hezbollah. Tare da taimakon tallafin Iran da horo da kuma makamai, ya saura ƙungiyar zuwa ta soji wadda hare-harenta suka tilasta wa Isra'ila kawo ƙarshen mamaya ta shekara 22 a kudancin Lebanon a 2000, wadda kuma ta yaƙi Isra'ila a yaƙin wata ɗaya a 2006.

Ga Isra'ila, kisan Nasrallah babbar nasara ce. A jawabinsa a babbar zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce "Isra'ila na samun nasara a yaƙinta da maƙiya da ke son tarwatsa ƙasar." Saboda haka ya bayar da umarnin kashe Nasrallah.

Firaministan Lebanon Najib Mikati ya ce kusan mutum miliyan ɗaya aka raba da gidajensu "saboda mummunan yaƙin da Isra'ila ta ƙaddamar kan Lebanon."

Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce sama da mutum 1,200 aka kashe, da suka kunshi yara da mata, a makwanni biyu.

Ƙoƙarin hana yaƙin ya cutura

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi maraba da kisan Hassan Nasrallah.

Kuma bayan soma mamayar, Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ya fitar da sanarwa yana mai cewa ya aminta da Isra'ila kan "buƙatar tarwatsa Hezbollah da lalata abubuwan more rayuwa a kan iyaka."

Sai dai Mr Austin ya jaddada cewa " akwai buƙatar maslaha ta fuskar diflomasiyya," domin tabbatar da kare fararen hula a dukkanin ɓangarorin biyu.

Wakilin BBC a ma'aikatar harakokin wajen Amurka Tom Bateman ya ce matakin Isra'ila na abka wa Hezbollah babbar ɓaraka ce ga tsarin shugaban Amurka Joe Biden na ƙoƙarin hana bazuwa yaƙin Gaza a yankin.

Biden ya ce zai ƙarfafa sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya, yayin da ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi gargaɗi ga mayaƙan da ke samun goyon bayan Iran kada su kuskura su kai wa sansanonin hari.

Hezbollah na nazari kan yadda za ta yi martani

Hezbollah tana da dubban mayaƙa, yawancinsu ƙwararrun mayaƙa ne a yaƙin basasar Syria, sannan tana da makamai masu linzami, galibinsu masu cin dogon zango da za su iya isa Tel Aviv da sauran birane.

Wakilin BBC kan tsaro Frank Gardner ya ce akwai matsin lamba a tsakanin shugaban ƙungiyar kan amfani da waɗannan makaman kafin a tarwatsa su, amma mummunan hari kan Isra'ila da zai kashe fararen hula zai iya haifar da mummunan martani.

Kisan Nasrallah babbar illa ce ga Iran, da kuma mayakanta waɗanda ke da tasiri a rikicinta da Isra'ila.

A ranar Lahadi, jirgin yakin Isra'ila ya kai hari a gine-gine a birnin Hudaydah a matsayin martani ga hare-haren makamai masu linzmi da mayaƙan Houthi suka kai mata.

Iran na iya ba mayaƙan Houthi da sauran mayaƙa a yankin umarni su ci gaba da kai hare-hare kan Isra'ila da sansanonin sojin Amurka. Amma duk martanin da za ta mayar, zai iya ƙara rura wutar barazanar yaƙi