Alex Ferguson zai bar matsayin wakilin Man Utd na duniya

t

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Sir Alex Ferguson zai bar matsayinsa na wakilin Manchester United a ƙarshen wannan kakar.

Manchester na biya Ferguson miliyoyin fan tun bayan murabus ɗin da yayi daga matsayin kocinta a 2013.

A wannan lokacin kocin mai shekara 82 na aiki a matsayin wakilinta na duniya kuma daraktan ƙungiyar.

Kullum yana zuwa kallon wasan ƙungiyar inda yake zama a wajen da darakta ke zama.

Majiyoyin ƙungiyar sun ce Ferguson wanda shi ne kocin da ya fi kowanne nasara a Manchester saboda Premier 13 da ya ci da Champions biyu da FA biyar da kuma Lig Cup hudu da dai sauransu, ya ce a koda yaushe aka neme shi a Old Trafford zai zo ya ba da ta shi gudunmuwar.

Kuma ya ce hukuncin da aka cimma an ɗauke shi ne bayan tattunawar fahimtar juna tsakaninsa da masu ƙungiyar Jim Ratcliffe a makon jiya.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Ratcliffe ke neman rage yawan kudaden da yake kashewa ya ƙara sa jari a cikin tawagar Man United.

Tuni aka sallami da ma'aikata sama da 250 daga aiki a wani mataki na rage yawan kudin da ƙungiya ke kashewa da fan miliyan 10.

A watan jiya United ta sanar da faduwar da ta yi ta fan miliyan 113. wanda ya yi kusa da asarar da ta yi a Premier Lig ta fan miliyan 115 cikin shekara uku, duk da cewa ƙungiyar ta ce tana ƙoƙarin ganin ta bi dokokin da aka shimfida ne a ko da yaushe.

A yanzu United na matsayi na 14 a teburin Premier, kocin ƙungiyar Erik ten Hag na nan kan matsayinsa na kocin ƙungiyar nan da zuwa ranar Asabar gabanin wasan Brentford, ko da yake ana ta yaɗa jita-jita kan makomar kocin.