Gabriel daga Chelsea ya koma Al-Nassr ta Saudi Arabia

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Brazil, Angelo Gabriel, wanda bai taɓa buga wa Chelsea babban wasa ba, ya koma babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia a Al-Nassr kan £19.1m.
Mai shekara 19 ya koma Stamford Bridge kan £13m a Yulin 2023 daga Santos, wanda ya buga wasannin aro a Strasbourg da yin karawa 24.
A Oktoban 2020 yana da shekara 15 da kwana 308, ya zama matashin farko a tarihin da ya fara buga gasar ta Brazil a lokacin da Santos ta fuskanci Fluminense a filin wasa na Maracana.
Matashin ɗan wasan zai taka leda tare da Cristiano Ronaldo da kuma Sadio Mane a Al-Nassr.
Shi kuwa Daniel Podenc ya koma Al-Shabab daga Wolverhampton Wanderers kan £5m.
Ɗan kasar Portugal, mai shekara 28, ya je Wolves tun daga 2019 da buga mata wasa 108 da cin ƙwallo 16.
Ya je ya yi wasan aro a tsohuwar ƙungiyarsa Olympiacos a kakar da ta wuce.
A yammacin Litinin aka rufe kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo a babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia.












