Halin da ake ciki a Tehran tun bayan fara hare-haren Isra'ila

Asalin hoton, ABEDIN TAHERKENAREH/EPA-EFE/Shutterstock
- Marubuci, BBC News Persian
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Isra'la ta farmaki Iran da manya-manyan hare-haren ta sama da ta ɗauki shekaru ba ta ƙaddamar da irin su ba.
Hakan ya ha da martani daga Iran, inda ƙasashen biyu suka ci gaba da musayar wuta tsakaninsu.
Aƙalla mutum 24 aka kashe a Isra'ila, kamar yadda ofishin yaɗa labaran firaminista Isra'ila ya bayyana.
Yayin da mutanen da aka kashe a Iran suka zarta 200, sakamakon hare-haren.
Al'umomin ƙasashen biyu na ci gaba da zama cikin ɗarɗar sakamkon hare-haren.
''Firgici'' ita ce kalmar da mutane da dama da BBC ta zanta da suke ke furtawa a Iran.
Wata mata ya shaida wa BBC cewa kwana biyu ba ta iya samun barci ba: ''Na shiga matsanancin yanayi.''
Ta ƙara da cewa halin da ake ciki yanzu a ƙasar ma tuna mata yaƙin Iran da Iraƙi da aka yi a shekarun 1980.
"Bambancin shi ne a wancan lokacin mukan ji ƙarar na'urar ankararwa a duk lokacin da aka kawo hari, amma a yanzu shiru kaka ji, saboda babu na'urorin'', in ji ta.
Matasan da aka haifa bayan wancan yaƙin, ba su san yanayi na yai ba, a cewar wakilin BBC na sashen Persian, Ghoncheh Habibiazad.

Asalin hoton, ABEDIN TAHERKENAREH/EPA-EFE/Shutterstock
Wani mazaunin birnin Tehran ya ce: "Dole na tuƙo motata daga wuri mai nisa domin na zo na sha mai a nan, a kowane gidan mai akwai dogayen layuka.
Wasu mutanen ma ficewa suke yi daga birnin na Tehran, ''musamman indai jami'ai ke zaune''.
Sadarwar intanet ta fara samun matsala, don haka tuntuɓar mutane ya fara zama da wahala a cikin ƙasar, a cewar wakilinmu.
Mutane da dama da ke zaune a wajen ƙasar na aike wa saƙonni ga ƴan'uwa da abokan arziki da ke zaune a birnin, tare da fatan samun amsa daga gare su.
Wata mata a Tehran na duba yiwuwar ficewa daga birnin domin kauce wa hare-haren.
"Muna son komawa ƙananan birane ko ƙauyuka, ko wasu wurare, to sai dai dukkanmu muna da mutanen da ba za su iya ficewa ba, kuma muna tunaninsu,'' in ji ta.
''Abin da ke faruwa a nan ba ya yi mana daɗi, mu mutanen Iran''.
Abin da gwamnati ke cewa

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani abu da ya fi firgita mutane a cikin Iran shi ne ruguza gidajen mutane, fiye da cibiyoyi nukiliya da sansanonin sojin sama, kamar yadda wakilin BBC Pouyan Kalani ya bayyana.
hare-haren sun sa mutane da dama da suka tsinci kansu cikin halin tsaka mai wuyar, aza ayar tambayar: ''Mene ne haƙiƙanin abin da ke faruwa, da adda yaƙin ya bazu, da yadda za su kare kansu da kuma iyalansu?
Jami'an Iran sun kasa yin bayanin abin da ya sa tsawon samanyar ƙasar ba ya aiki, har ta kai Isra'ila ta far wa muhimman wrare a ƙasar cikin sa'a guda.
Sa'o'i bayan harin Isra'ila na farko da tsakar daren ranar Juma'a - har ma kusan kwana guda -babu hukumar gwamnati a Iran da ta yi ckakken bayanin da zai taimaka wa mutanen sanin girman ɓarnar da harin ya haddasa ba, da kuma yadda za a mayar da martani.
Inda mutane da dama suka ci gaba da tambayar: Shi ƙasar ta faɗa yaƙi ne?
Sai dai duka mutanen da suka bayyana a talbijin suka yi bayani, sun ce ''babu wani babban abu da harin ya haifar, inda suka dage cewa sun magance komai, kuma biranen ƙasar na cikin amince.
Babu wani bayani daga hukumomi kan yadda jiragen yaƙin Isra'ila suka shiga ƙasar zuwa Tehran da sauran wasu biranen ba tare da fuskantar turjiya ba.

Asalin hoton, WANA/Reuters
Sai dai da rana bayan hare-haren, jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana gidan talbijin na ƙasar inda ya yi wa ƙasar jawabi
Cikin jawabin nasa, Ayatollah Ali Khamenei, bayyana cewa sojjin ƙasar za su yi amfani da ƙarfi domin tabbatar da cewa gwamnatin Yahudawa ta ɗanɗana kuɗarta''.
Zuwa da maraice, Iran ta ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami zuwa birnin Tel Avin na Isra'ila, inda kuma kafofin yaɗa labaran gwamnatin Iran suka fara yaɗa hare-haren kai tsaye, inda suka riƙa nuna abin da ke faruwa a birnin Tel Aviv.
Sa'o'i bayan hakan, ministan cikin gidan Iran ya yi wa ƴan ƙasar jawabi a gidan talbjin na ƙasar, yana mai kiran mutane su kwantar da hankula, tare dakauce wa tafiye-tafiyen da ba su zama dole ba, da bai wa jami'a haɗin kai.
Baya ga bayayna mutuwa manyan kwamandojin dakarun juyin-juya halin Iran da ƙwararrun masani kimiyya, sauran bayanan sun fito ne daga wasu kafofin yaɗa labaran ƙasar.
Inda aka kasa samun cikakkun bayanan hare-hare kan sojoji da cibiyoyin nukiliyar ƙasar, da kuma haƙiƙanin alƙaluman waɗanda suka mutu.
To sai dai duka da cewa daga baya bayani sun fito, har yazu babu cikakkun bayanai kan yadda hare-haren suka auku da adadin jami'ai da ƙwararrun kimiyyar da aka kashe, da kuma fararen hula da suka mutu sakamakon hare-haren.












