Yadda kisan Chirlie Kirk ya fito da rarrabuwar kai a Amurka

    • Marubuci, Katty Kay
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, US Special Correspondent
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Batun kisan wani babban mai kare manufofin Trump a Amurka a makonnin da suka gabata ya haifar da ayar tambayar cewa shin ko Amurka ne neman zama ƙasa mafi hatsari a duniya?

Bayan ɗaya daga cikin kisan gilla da aka yi a tarihin ƙasar, gwamnan jihar Utah ya roƙi Amurkawa su yi watsi da yanayin siyasar ƙasar.

Amma da wahala duk wanda na yi magana da shi tun mutuwar Charlie Kirk ya yi tunanin hakan zai zama hanyar da ƙasar za ta zaɓa.

Abin da ya faru na kisan Kirk misali ne yadda Amurkawa ba sa nuna hadin kai a lokacin da wani bala'i ya faru.

Irin hakan ta faru kimanin shekara 14 da suka wuce lokacin da aka harbe ƴar majalisar wakilai ta jam'iyyar Democrats a jihar Arizona.

Haka a shekara takwas da suka wuce aka kashe ɗan majalisar Repblican a lokacin atisayen wasan baseball.

Amurkawa ba su cika fitowa fili su haɗa kai a lokacin faruwar wani bala'i ba.

Hatta annobar Covid sai da ta haifar da rarrabuwar kawuna a ƙasar.

Wannan al'amari yana da wuyar canzawa, saboda masu ƙarfafa wa waɗanda ke rura wutar rayuwar siyasar ƙasar suna bai wa mutane damar ci gaba da yin hakan.

A duk faɗin Amurka, za ka iya samun damar a zaɓeka kowane matsayin siyasa, idan ka yi aiki a kan manufofi da maganganun da ke jan hankalin siyasarku, maimakon manufofin wasu.

Haka ma a kafofin yaɗa labarai, Mutane masu ra'ayin siyasa na samun damar a yaɗa labaransu.

Bayan an kashe Charlie Kirk, gwamnan Utah ya umarci Amurkawa su riƙa taka tsanta tare da kula da iyalansu, sannan su riƙa mu'amala mai kyau idan sun fita waje.

Ya yi magana cikin taushi da nufin magance bambance-banbamcen ra'ayi da ke tsakanin Amurkawa

Kwatanta shekarun 1960 da 1970 da yanzu

Rarrabuwar kawuna da rikicin siyasa ba sabon abu ba ne a Amurka, lamarin ya samo asali ne tun a shekarun 160.

A cikin shakara biyar a cikin shekarun 1960, an kashe shugaban Amurka da ɗan'uwansa a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar.

A dai wanann lokacin aka kashe biyu daga cikin fitattun shugaban gwagwarmayar kare yanci.

Haka ma a 1970, aka harbi shugaba Gerald Ford har sau biyu a mabambantan lokuta.

A shekarun 1980 aka harbi Ronald Reagan da bindiga, yayin da yake tafiya a cikin motarsa.

Ta ya za a magance matsalar?

Game da tambayar da wasu ke yi kan yadda za a rage wannan matsala ta rarrabuwar kawuna, ana buƙatar jajirtaccen shugaba mai ƙarfin faɗa a ji da ya sanya magance matsalar a gabansa.

"Ban san yadda za mu magance wannan ba," a cewar marubucin siyasa, David Drucker.

"Za a iya magance matsalar idan duka ɓangarorin - ɓangare nake nufi ba jam'iyya ko ƴansiyasa ba - sun amince da dakatar da irin wannan bambancin.

"A ƙa'ida ya kamata a ce shugaban ƙasar ne zai yi hakan. Idan duka ɓangarorin suka ƙi amincewa akwai gyaran da ba zai yiwu ba, kuma idan har shugaban ƙasar ya kasa yi, to bana tunanin akwai wanda zai iya yi ."

Trump ba irin shugabannin da zai iya kawo gyaran ba ne. A wasu lokuta ana ganin yana da ƙarfin siyasa idan da zai ɗauki ƙudirin yaƙi da ɗabi'ar.

Abin da na fahimta shi ne Trump ya yi imanin cewa mutane da ke hammaya da shi na son kawo wa tafiyarsa nakasu.

Kuma tun bayan mutuwar Kirk ya riƙa kausasa murya dangane da kalaman gwamnan Utah.

"Zan gaya muku wani abu da wataƙila ba zai yi muku daɗi ba, amma gaskiyar magana ba zan iya gyara matsalar nan ba," in ji shi, lokacin da aka tambaye shi yadda za a magance matsalar.

"Masu tsattsauran ra'ayi a dama sau da yawa suna ɗaukar ra'ayi mai tsanani saboda ba sa son ganin ana aikata laifin ... Masu tsattsauran ra'ayi a gefe guda su ne tushen matsalar."

Haka a ranar 11 ga watan Satumba cikin jawabin da ya yi a aofishinsa kan kisan Kirk ya ce ''ƴansiyasa masu tsattsauran ra'ayi da ke ingiza rikici na cutar mutane da dama da ba su ji ba su gani ba ta hanyar kashe su.''

To sai dai akwai bincike masu yawa da ke nuna cewa siyasa ce ke haifar da matsalar kashe-kashe da rikice-rikice a Amurka, cikin gomman shekaru.

'Tarihi ne ke maimata kansa'

Wasu mutane da na yi magana da su sun nuna cewa dama tun asali haka Amurka ta gada.

To sai dai gaskiya ba haka lamarin yake, dole akwai mafarin kowane abu.

"Lokuta ƙalilan ne aka samu ire-iren waɗannan matsaloli idan ka kwatanta da lokutan da ba a samu matsalolin ba''.

''A cikin shekarun 1960 da farkon 1970, Vietnam da Watergate suka yi wani yunƙurin rage matsalar," a cewar tsohon ɗan majalisar Republican Joe Scarborough.

"Yunƙurin ya samu ci gaba dangane da raguwar matsalar''.

Har ila yau, a cikin waɗanda na zanta da su akwai Sanata Raphael Warnock na jam'iyyar Democrat daga Georgia, ɗaya daga cikin manyan jami'ai baƙar fata a ƙasar.

Ya yi Allah-wadai da tashe-tashen hankula na siyasa a matsayin abin da ya fi dacewa da tsarin dimokradiyya, amma kuma ya tunatar da ni irin ci gaban da Amurka ta samu kan batutuwa ƙyamar launin fata.

"Labarin kowane dangi na da sarƙaƙiya fiye da labaran da muke faɗa wa kanmu a lokacin taron ganawa da iyali'', kamar yadda ya shaida min.

"Duk da mahaifina soja ne ya taɓa haƙura ya bai wa wani matashi kujerarsa a cikin motar bas, amma yanzu ni ɗan majalisar dattawa ne''.

Suna cike da fatan samun sauƙi, ai dai yanzu babu alamar hakan.