Babu matsala tsakanina da Perez don an fitar da mu a Champions League - Ancelotti

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Carlo Ancelotti ya ce bai samu rashin jituwa da Florentino Perez ba, bayan da aka fitar da Real Madrid a Champions League ranar Laraba.

Arsenal ce ta yi waje da Real Madrid a gasar zakarun Turai zagayen kwata fainal ta bana, hakan ya sa ake ta jita-jita kan makomar kociyan mai shekara 65.

Sai dai kafin wasan da Real za ta kara da Athletic Bilbao ranar Lahadi a La Liga, Ancelotti ya sanar cewar ba shi da wata matsala da shugaba, Perez.

Real Madrid mai rike da kofin La Liga na bara tana ta biyu a teburi da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona mai jan ragama.

Ranar 26 ga watan Afirilu za a fafata a wasan karshe a Copa del Rey tsakanin Barcelona da Real Madrid.

''Champions League babban kofi ne da yake da mahimmaci ga kowo'', in ji Ancelotti. ''Kuma Real tana da babban tarihi a gasar zakarun Turai.''

Ancelotti, wanda ya lashe Champions League karo uku ya kara da cewa ''Abin da ya baƙanta min rai irin caccakar ƙwazon Real da ni kaina, bayan da Arsenal ta kai zagayen gaba da cin 5-1.

Ƙwantiragin Ancelotti a Real Madrid zai kare a karshen kakar 2026, ya kuma ce zai tattauna da Perez a karshen kakar nan, domin fayyace makomarsa.

Sai dai bai fayyace lokacin da zai gana da shugaban Real ba, watakila kafin ko kuma bayan watan Yuni lokacin Club World Cup a Amurka da Real za ta buga gasar.

An yi ta alakanta kociyan ɗan kasar Italiya da aikin horar da Brazil, bayan da aka kori Dorival Junior, sakamakon da Argentina ta ci Brazik ƙwallaye da yawa.

Ranar Juma'a kociyan Bayern Leverkusen, Xabi Alonso ya ce ba lokaci ne da ya dace ake maganar makomarsa ba, wanda ake dangan ta shi da aikin horar da Real Madrid.